--
An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a

An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a



A kalla mutane takwas aka raunata yayin wani rikici da ya barke a tsakanin mabiya darikun addinin Musulunci biyu a kan jagorantar Sallah a babban Masallacin garin Okene da ke jihar Kogi.

Kafin wannan rikicin, da ma can akwai wata jikakkiya a tsakanin mabiya Tijjaniyya da Sunni a kan wanda zai gaji kujerar babban limamin Masallacin, Alhaji Musa Galadima,:

wanda ya mutu a cikin watan Afrilu na shekarar 2019. Shaidar gani da ido ya ce rikicin ya samo asali ne bayan wani dan Izala mai suna Mallam Bello Hussaini ya kira limamin Masallacin, Sheikh Salihu, da mukaddashin liman yayin da ya shigo Masallacin.

Kalaman mabiyin Izalar sun fusata wani mabiyin Tijjaniyya mai suna Momoh Jimoh, wanda ya bukaci Malam Hussaini ya nemi afuwar babban Liman a kan cin fuskar da ya yi masa. Shaidar ya sanar da 'TheNation' cewa lamarin ya haifar da hargitsi tare da yi wa Jimoh mugun duka tare da ji masa rauni a ka.

Ana zargin 'yan Izala ne da yi masa dukan. Faruwar hakan ta haifar da bawa hammata iska a tsakanin mabiya darikun guda biyu, lamarin da ya sa wasu Masallatan tserewa daga Masallacin. An shafe kusan sa'a guda ana rikici kafin daga bisani 'yan sanda da sojoji su kwantar da tarzomar.

Sai dai, kafin zuwan jami'an tsaron, a kalla mutane takwas ne su ka samu raunuka daban - daban yayin rikicin. Abdulsalam Mohammed Bashir, wani ma'aikacin gwamnati da ya ke Masallacin a lokacin rikicin ya faru, ya bayyana abin da mai ban takaici.

"Ina cikin Masallacin lokacin da Sheikh Salihu Abere, babban liman, ya shigo domin jagorantar Sallar Juma'a. "Mutane da yawa sun yi mamaki a lokacin da Bello Hussaini ya dakatar da fadakarwa tare da sanar da cewa mukaddashin Liman,


Sabanin babban Liman, ya shigo Masallaci. "Hakan ne ya haddasa rikicin da ya jawo aka raunata Ibrahim Ochi, Ibrahim Ojivo, Momoh Jimoh da sauransu," a cewarsa. Da ya ke mayar da martani a kan faruwar lamarin, Ustaz Bello Hussaini, wanda ake zargi da haddasa rikicin,

ya ce a gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ne ya nada Sheikh Salihu a matsayin mukaddashin liman a shekarar 2019. Ya kara da cewa tun daga wancan lokacin, babu wani sabon umarni da ya nuna an tabbatar da Sheikh Salihu a matsayin liman mai cikakken iko.

Gwamna Yahaya Bello ya gayyaci babban sarkin kasar Ebira tare da sauran wasu manyan fadarsa biyar zuwa gidan gwamnatin jihar Kogi da ke Lokoja domin nemo mafita ga lamarin.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANANhttps://www.bzglobalservice.com.ng/

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An raunata mutane 8 yayin rikici tsakanin 'yan Izala da Tijjaniyya a kan limancin Masallacin Juma'a "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?