--
Yahaya Bello ya saka a binciki kwamishinan da ake zargin ya yiwa wata budurwa fyade

Yahaya Bello ya saka a binciki kwamishinan da ake zargin ya yiwa wata budurwa fyade

- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya bada umarnin bincikar kwamishinan ruwan jihar sakamakon zargin da ake mishi

- Wata budurwa mai suna Elizabeth Oyeniyi ta zargi kwamishinan da yi mata fyade tare da cin zarafinta bayan wata wallafa da tayi a shafinta na Facebook - Gwamnan ta hannun kwamishinan yada labarai na jihar ya ce ba za su lamunci cin zarafin mata da kananan yara ba Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya bada umarnin bincikar daya daga cikin kwamishinonin shi,

Abdulmumin Danga wanda ake zargi da fyade da cin zarafi. Gwamna Yahaya Bello ya bada umarnin ne na cewa a gaggauta bincikar kwamishinan sakamakon zarginsa da ake da fyade da kuma cin zarafi.

Yahaya Bello ya saka a binciki kwamishinan da ake zargin ya yiwa wata budurwa fyade Source: Facebook 

A wata takarda da ta fita a garin Lokoja, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ya ce gwamnan ya bada umarnin bincike a kan lamarin don tabbatar da wanzuwar adalci.

"A matsayin gwamnan na jakaden bin hakkin bil Adama, ya sha matukar mamaki a kan zargin, hakan yasa ba zai bar lamarin ba ba tare da an bincika ba. "Gwamnan ya bada umarnin bincikar lamarin da gaggawa. Ya bada tabbaci ga mai zargin, wanda ake zargin da kuma jama'a baki daya cewa za a gano gaskiyar lamarin sannan a dau matakin adalci.

"Ba zamu lamunci cin zarafi ga yara da mata ba ta kowacce fuska. Muna tabbatar da cewa za a binciki zargin kuma duk wanda aka kama da laifi zai fuskanci hukunci," Kwamishinan yace. Idan za mu tuna, shafin Linda Ikeji ya ruwaito yadda wata budurwa mai suna Elizabeth Oyeniyi da ke jihar ta bayyana cewa Danga ya ci zarafinta tare da yi mata fyade a kan wallafar da tayi a shafinta na ranar 29 ga watan Maris.

Oyeniyi ta wallafa shawara ne ga kwamishinan a kan cewa ya fara wadata 'yan uwanshi kafin ya fito yana yi wa na waje. Ta ce hakan ya matukar harzuka kwamishinan don ya aiko 'yan daba inda suka dauketa da karfin tsiya har gaban shi. Bayan mugun dukan da ta sha, ya yi mata fyade da dare.


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Yahaya Bello ya saka a binciki kwamishinan da ake zargin ya yiwa wata budurwa fyade"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?