--
Tashin hankali: Jami'in gwamnati ya bayyana adadin mutanen da su ka mutu a cikin sati daya a Kano

Tashin hankali: Jami'in gwamnati ya bayyana adadin mutanen da su ka mutu a cikin sati daya a Kano



Har yanzu rahotanni na cigaba da bayyana yadda ake cigaba da samun yawaitar mutuwar mutane a Kano duk da tabbacin da gwamnati ta bayar na cewa ta shawo kan lamarin. A ranar Lahadi ne kwamishinan yada labarai a jihar Kano, Muhammad Garba, ya bukaci jama'a su kwantar da hankulansu tare da basu tabbacin cewa nan bada dadewa ba gwamnati za ta warware matsalar.

 Mutane da dama sun mutu a cikin mako guda a jihar Kano. A cewar Sabitu Shaibu, mataimakin shugaban kwamitin ko ta kwana a kan annobar covid-19 a jihar Kano, ya ce adadin mutanen da su ka mutu a Kano ya kai 640, kamar yadda jaridar 'TheCable' ta rawaito. Wasu na zargin cewa annobar cutar covid-19 ce ke hallaka mutane a Kano. Sai dai, a cewar Garba, mutane na mutuwa ne daga cututtuka irinsu hawan jini, zazzabi, ciwon sukari da sauransu.

Kazalika, mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya tabbatar da cewa ba annobar covid-19 ce ke hallaka mutane a masarautarsa ba, kamar yadda wasu su ke zargi.

A cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, Sarkin ya ce ma'aikatar lafiya ta jiha ta sanar da fadarsa cewa asarar dumbin rayukan da ake yi, ba sanadiyyar barkewar annobar cutar covid-19 bane. Ya yi addu'ar Allah ya ji kan wadanda su ka mutu tare da yi wa marasa lafiya fatan samun sauki. Da ya ke magana a kan annobar cutar covid-19, sarki Aminu ya yi kira ga mazauna Kano da su yi aiki da shawarwarin da hukumar yaki da cututtuka ma su yaduwa ta kasa (NCDC) ta bayar a kan dakilye yaduwar covid-19.

Annobar yawaitar mace-mace ta lakume rayukan fitattun mutane a Kano da suka hada da manyan malaman jami'a da suka kai matakin Farfesa. An sanar da mutuwar tsohon kwamishinan ilimi a jihar Kano, Aminu Yahaya, da Farfesa Balarabe Maikaba, a ranar Lahadi. Mudi Mudi, babban jami'i a hukumar kula da makarantun sakandire ta Kano (KSSMB) ya mutu ranar Lahadi. Asarar rayukan ba a iya kan fitattun mutane ta tsaya ba,

 dumbin talakawa sun mutu a Kano a 'yan kwanakin baya bayan nan. Ministan lafiya, Osagie Enahire, ya ce gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zai binciko musabbabin yawaitar mutuwar mutane a Kano. Kazalika, Femi Falana, babban lauya mai rajin kare hakkin bil'adama, ya bukaci gwamnatin tarayya ta sanar da jama'a sakamakon binciken kwamitinta da zarar kwamitin ya mika mata rahotonsa.

 KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "Tashin hankali: Jami'in gwamnati ya bayyana adadin mutanen da su ka mutu a cikin sati daya a Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?