LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Shekau ya saki sabon sako bayan sojojin kasar Chadi sun kashe masa dumbin mayaka

Bayan mayakan kungiyar sun kai wa dakarun sojin kasar Chad harin kwanton bauna a cikin makon da ya gabata, dakarun sojojin kasar ta Chadi sun kai wa mayakan kungiyar Boko Haram harin ramuwar gayya. A yayin da yake ganawa da kwamandojin rundunar sojojin hadin gwuiwa (MNJTF) a Baga ta jihar Borno bayan harin daka kai wa sojojin kasarsa,

shugaban kasar Chadi, Idriss Derby, ya bawa sojojin umarnin su fara wani atisaye, ba tare da nuna tausayi ba, a yankin tafkin tekun Chadi. A wani faifan bidiyo da PRNigeria ya samu, an ga sojojin kasar Chadi suna wakokin karawa junansu karfin gwuiwa yayin da suke harbawa mayakan kungiyar Boko Haram makami mai nisan zango (RPG) a lokacin da suke kazamar musayar wuta.

A wani faifan bidiyon na daban, an ga dakarun sojojin na kasar Chadi suna tattaka mayakan kungiyar Boko Haram da suka zube a kasa jina-jina da kuma wadanda suka mutu bayan an fafata musayar wuta a tsakani. Kalli faifan bidiyon a kasa:

LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YKU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
b

Post a comment

0 Comments