--
Fursunonin da aka yi wa afuwa sun yi kadan — Shehu Sani

Fursunonin da aka yi wa afuwa sun yi kadan — Shehu Sani


Gwamnatin Najeriya ta ce ta yi wa fursunoni 2600 afuwa a wani mataki na hana cunkoso a wannan lokaci da kasar ke yaki da annobar coronavirus.

Sai dai sakin fursunoni ya janyo ce-ce-kuce tsakanin masu kare hakkin bil adama, ko da ya ke wasu sun yaba da matakin.

Sanata Shehu Sani, da ke fafutukar rajin kare hakkin bil adama ya ce idan akayi la'akari da cunkoson gidajen yarin Najeriya, kamata ya yi a ce kusan kashi 50 na fursunoni aka sallama.

Tsohon Sanatan da shi ma a baya ya taba zama a gidan yarin kasar, ya ce halin da gidan yarin kasar ke ciki ya wuce misaltuwa, akasari zama ake a cakude babu walwala.
Ya ce ''Duk abubuwan da ya kamata a ce akwai a kurkuku babu su, sannan tsarin irin na turawan mulkin mallaka ne babu wani abu sabo a ciki''.

Sannan '' Hatta dokokin gidan yarin ba su sauya ba, da tsarin cin abinci, haka babu sabbin gine-gine.''

A ranar alhamis ministan harkokin cikin gidan kasar, Rauf Aregbesola ya ce cikin fursunonin da aka saka akwai 70 daga gidan yarin Kuje da ke Abuja, sannan daga bisani a saki sauran fursunonin.

Fursunonin sun hada da tsofaffi da marasa koshin lafiya da masu tabin hankali da kuma wadanda aka ci tarar su kasa da N50,000.

Sa dai ya ce ba za a saki wadanda aka kama da laifin ta'addanci da satar mutane da kisa ba.

Shehu Sani ya ce ba wai Najeriya ba ce kawai ta dau irin wannan mataki akwai kasashe da dama da suka dau irin wannan mataki.

Kuma a cewarsa, sakin fursunoni a wannan lokaci lalura ce da ta zama tilas ganin halin da kasar ke ciki dama duniya.

Sai dai sanatan, ya ce kawai matsalar da aka samu ita ce ta adadin fursunonin da bai taka kara ya karya ba, ganin yawan mutanen da ke tsare.

Ya ce, ''Kurkuku wuri ne da ake tsare mutane da yawa idan aka bari mutum daya ya kamu da wannan cuta to sai ya yada ta ga kowa''.
Kuma ''Ya kamata duk mutumin da ya yi rabin shekarun da aka yanke masa a sake shi, wadanda kuma har yanzu ba a kai ga kai su kotu ba ya kamata a sake su.'' inji Sanatan.

Kin daukan wannan mataki zai haifar da cikas a kokarin cimma manufofin gwamnati na yakar wannan annoba kamar yadda sanatan ya ce.

Karin bayani
Gwamnati dai ta ce adadin fursunonin da ta yi wa afuwa ba su yi kadan ba, saboda tsari ne da za a ci gaba ba wai na lokaci guda ba.
Najeriya dai na da fursunoni sama da dubu 80 a gidajen yari 250 da ke fadin kasar, cikinsu kuma dubu 50 na jiran shari'a.

Kuma ana yawan samun korafi kan yanayin gidajen yarin da kuma yadda ake tsare da fursunoni.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun sha sukar yanayin fursunonin kasar da kuma yadda ake tsare mutum na tsawon lokaci ba tare da an yi masa shari'a ko yanke hukunci ba.

Fursunonin da aka yi wa afuwa a wannan lokaci sun shaida wa BBC halin farin cikin da suka tsinci kansu, wasu kuma sun yi nadamar laifukan da ya kai ga garkame su.KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Fursunonin da aka yi wa afuwa sun yi kadan — Shehu Sani"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?