--

Covi-19: Idan mutum ya warke daga Coronavirus ba zai sake iya kamuwa da cutar ba - Masani ilmin kwayoyin cuta

Covi-19: Idan mutum ya warke daga Coronavirus ba zai sake iya kamuwa da cutar ba - Masani ilmin kwayoyin cuta



Wani Malami kuma masanin ilmin kwayoyin cuta, Farfesa Sunday Omilabi, ya bayyana cewa duk wanda ya samu warkewa daga cutar Coronavirus ya samu wani irin garkuwar jiki mai karfi.

Wannan garkuwa jiki za ta kareshi daga iya sake kamu da cutar a nan gaba.

Farfesa Omilabu, wanda ma'aikaci ne a asibitin koyarwan jami'ar Legas, Idi Araba, ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a hirar da yayi da mambobin kungiyar marubuta labaran kiwon lafiya a Najeriya wato Health Writers’ Association of Nigeria (HEWAN).

A cewarsa, idan mutum ya warke daga cutar, hakan na nufin cewa ya samu wasu sabbin garkuwan jiki isassu.

Yace “Har yanzu bamu samu labarin wanda ya warke da ya sake kamuwa da cutar ba ko wani sashen jikinsa ya lalace ba.“

“Kuma ban tunanin akwai wani nakasa da mutum zai samu saboda muddin mutum ya tsira daga COVID-19, zai kara karfi.“

“Ana kyautata zaton cewa mutum kara samu garkuwan jiki masu karfi.“

“Yawancin wadanda aka sallama daga asibiti sun yi gwaji akalla sau biyu wanda ya nuna cewa sun warke kuma yawunsu bai dauke da kwayar cutar ko daya.“

“Saboda haka babu wani tsoron mutum zai iya sake kamuwa, amma muna bukatar karin bincike kafin iya yanke haka.“

Farfesa Omilabu ya yi kira ga yan Najeriya su tsafta tare da baiwa juna tazara domin taimakawa gwamnati wajen yakar cutar Coronavirus.

A bangare guda, Olorunnimbe Mamora, karamin ministan lafiya na kasar nan yace bai san abinda ya warkar da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ba daga cutar coronavirus da ta kama shi.

A ranar Laraba ne Mamora ya bayyana hakan ga kwamiti na musamman na shugaban kasa a kan cutar, a babban birnin tarayyar Abuja.

Mamora ya ce, "Ban san yadda aka yi mai girma gwamnan jihar Oyo ya warke daga cutar coronavirus ba".

Ya ci gaba da cewa, "Ban san a asibitin da aka kaishi har ya karba magani ba. Zan so in samu bayanan don in fitar da takardar".KARANTA WASU LABARI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/


LATSA NAN๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP
https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 






Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

KUSAUKE MANHAJAR LABARAI A WAYOYINKU NA ANDROID KYAUTA LATSA LINK DIN RUBUTUN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU
https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Covi-19: Idan mutum ya warke daga Coronavirus ba zai sake iya kamuwa da cutar ba - Masani ilmin kwayoyin cuta"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?