--
Coronavirus: An umarci jami’an tsaro su bindige masu kunnen-kashi a Philippines

Coronavirus: An umarci jami’an tsaro su bindige masu kunnen-kashi a Philippines

Shugaban Philippines, Rodrigo Duterte, ya yi gargadin cewa za a iya harbe mutane idan suka tayar da yamutsi saboda dokar takaita zirga-zirgar da aka sanya saboda coronavirus.

A jawabin da ya yi a gidan talbijin, Shugaba Duterte ya ce 'yan sanda da sojoji suna da ikon harbi idan suka ga rayuwarsu ta fada cikin hatsari.

Ya yi gargadin ne bayan 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar neman tallafin abinci a birnin Manila.

Da ma dai ana zargin Shugaba Duterte da aiwatar da dokar kashe mutanen da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi ba tare da an yi musu shari'a ba.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce bai kamata a rika yin amfani da karfin da ya wuce kima ba wajen tursasa wa mutane bin dokar hana fita.

Article share tools


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




Domin Magana Damu Ko Bamu Shawara Ko Turo Mana Da Labari Ku Latsa Link Din Dake Qasa Domin Magana Damu Kaitsaye Ta whatsaapp👇👇👇https://wa.me/2349066633320?text=Assalamu'alaikum%20Bz.%20Barka%20Da%20Aiki%F0%9F%A5%B0%F0%9F%A4%9D

0 Response to "Coronavirus: An umarci jami’an tsaro su bindige masu kunnen-kashi a Philippines"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?