--

An sake tafka rashin wani babban Farfesa a jihar Kano

An sake tafka rashin wani babban Farfesa a jihar Kano

Balarabe Maikaba, Farfesa a bangaren ilimin aikin jarida a jami'ar Bayero ta Kano, ya mutu ranar Lahadi. Wata majiya mai kusanci ga marigayi Maikaba ta sanar da jaridar 'TheCable' cewa za a yi jana'izarsa bayan sallar La'asar a birnin Kano. Wani tsohon dalibin Farfesa Maikaba ya shaidawa 'Thecable' cewa ya kammala shiri tsaf domin halartar jana'izarsa da za a yi a unguwar Fagge da ke cikin garin Kano.

Maikaba ne Farfesa na shidda da ya mutu a jihar Kano a cikin sati guda. Ana fama da yawaitar mace-macen jama'a a 'yan kwanakin baya bayan nan a jihar Kano. Legit.ng ta wallafa rahotanni a kan yadda jama'ar Kano ke zaune cikin zulumi sakamakon yawaitar mutuwar mutane, yawancinsu dattijai.

Legit.nt ta wallafa rahoton labarin mutuwar Fitaccen masanin ilimin tattalin arziki, Farfesa Ibrahim Ayagi, wanda ya mutu ranar Asabar a jihar Kano. An haifi marigayi Ayagi a shekarar 1940 a jihar Kano, ya mutu yana da shekara 80 a duniya bayan ya sha fama da rashin lafiya.

An yi jana'izarsa bayan sallar La'asar a gidansa da ke kallon makarantar sakandiren Gwale a cikin garin Kano. Marigayi Ayagi, wanda ake girmamawa saboda iliminsa a bangaren tattalin arziki, ya taba rike babban darektan bankin 'Continental Merchant Bank'. Farfesa Ayagi ya taba rike kujerar kwamishinan cigaban tattalin arzikin jihar Kano daga shekarar 1975 zuwa 1978.

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/



KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: BZGLOBALSERVICE.COM.NG APP

0 Response to "An sake tafka rashin wani babban Farfesa a jihar Kano"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?