--
Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 20 sun kamu da cutar Coronavirus, Legas Abuja da Kaduna

Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 20 sun kamu da cutar Coronavirus, Legas Abuja da Kaduna



Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane ashirin da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya. Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Litinin inda tace: “An tabbatar da mutane ashirin sun kamu da #COVID19

a Najerya. 13 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Kaduna, .“ “Dai-dai Karfe 9:o0 na daren 30 ga Maris, mutane 131 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami takwas, kuma biyu ya rigamu gidan gaskiya.“ Ga jerin jiha-jiha Lagos- 81 FCT- 25 Ogun- 3 Enugu- 2 Ekiti- 1 Oyo- 8 Edo- 2 Bauchi- 2 Osun-2 Rivers-1 Benue- 1 Kaduna- 3

Mun kawo muku rahoton cewa Uwargidar Malam Nasir El-Rufai, Hadiza Isma-El-Rufai ta shaidawa Duniya cewa ta ta yi gwajin wannan cuta mai yawo. Amma ba a ji labarin sakamakon ba tukuna.

Hajiya Hadiza Isma-El-Rufai ta yi wannan bayani ne a shafinta na sada zumunta na Tuwita. Mai dakin gwamnan ta kuma godewa addu’o’in da jama’a su ke yi masu. Hadiza El-Rufai ta nuna cewa Gwawnan ya na ta fama da zaman kadaici na kebewa sauran jama’a,


domin gudun yada wannan mummunar cuta ga sauran Bayin Allah. Isma-El-Rufai ta ce: “Nagode Jama’an Tuwita da duka addu’o’i da fatan alherinku. Mai girma gwamna ya na samun lafiya.” Har yanzu cutar ba ta fara bayyana a jikinsa ba. Daga baya yau za a yi mani gwaji. Ina sa ran ganin alheri. A halin yanzu mu na cigaba da zaman kebewa jama’a.”
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "Yanzu-yanzu: An samu karin mutane 20 sun kamu da cutar Coronavirus, Legas Abuja da Kaduna "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?