--
Yanzu-yanzu: Mutane 14 sun sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya, jimilla 111

Yanzu-yanzu: Mutane 14 sun sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya, jimilla 111



Hukumar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karuwar mutane 14 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya. Hukumar ta bayyana hakan a shafin raayinta na Tuwita ranar Lahadi inda tace: “An tabbatar da mutane 14 sun kamu da #COVID19 a Najerya.

5 a Abuja, 9 a Legas.“ “Dai-dai Karfe 9:30 na daren 28 ga Maris, mutane 97 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami uku, kuma daya ya rigamu gidan gaskiya.“ Ga jerin jiha-jiha Lagos- 68 FCT- 21 Oyo- 7 Ogun- 3 Enugu- 2 Edo- 2 Bauchi- 2 Osun-2 Ekiti- 1 Rivers-1 Benue- 1 Kaduna- 1

Yanzu-yanzu: Mutane 14 sun sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya, jimilla 111 Source: Twitter A bangare guda, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya dokar hana fita a birnin tarayya Abuja, da kuma jihohin Ogun da Legas, na tsawon makonni biyu domin takaita yaduwar cutar Coronavirus.

Ya sanar da hakan ne a jawabin da ya yiwa yan Najerya da yammacin Lahadi, 29 ga Maris, 2020. A cewarsa, dukkan mazaunan wadannan jihohi su kasance cikin gidajensu kuma su guji tafiya zuwa wata jiha. Amma ya togaciye wani bangaren mutane da ya hada da yan kasuwa masu sayar da kayan abinci, kamfanonin man fetur, ma-aikatan wutan lantarki da jamian tsaro masu zaman kansu.

Hakazalika kamfanonin sadarwa, da kuma yan jaridan da ba zasu iya aiki daga gida ba. Yace “Bisa ga shawarar maaikatar kiwon lafiya da hukumar NCDC, ina bada umurnin hana hada-hada a Legas da birnin tarayya na tsawon kwanaki 14 fari daga karfe 11 na dare na ranar Litinin, 30th ga Maris, 2020.“

“Wannan dokar hana fitar za ta shafi jihar Ogun saboda kusancinta da jihar Legas da yawan tafiye-tafiyen da ake tsakaninsu.“ “Lallai mun san wannan mataki zai tsanantawa mutane da dama, amma wannan lamarin rayuwa ko mutuwa ne idan muka lura da irin yadda ake mutuwa kullum a Italiya, Faransa da Andalus.“


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "Yanzu-yanzu: Mutane 14 sun sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya, jimilla 111 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?