Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Friday, March 13, 2020

  Yanzu-yanzu: Cristiano Ronaldo baya dauke da Coronavirus  - Cristiano Ronaldo baya dauke da coronavirus

  - Shugaban gwamnatin Madeira Alberquerque ne ya tabbatar da hakan

  - An killace Ronaldo saboda domin yi masa gwaje-gwaje

  Sakamakon gwaje-gwaje da aka gudanar ya nuna cewa Cristiano Ronaldo baya dauke da cutar Coronavirus mai hatsari bayan an killace shi a kasar Portugal tun farkon wannan makon.
  Miguel Albuquerque, shugaban gwamnantin Madeira ne ya yi wa Daily Mail wannan jawabin wanda ke nuna Cristiano Ronaldo lafiyar shi kalau a yanzu.
  Wannan sakamakon zai zama abin farin ciki ga Cristiano Ronaldo da iyalansa da masoyansa a fadin duniya da suke nuna damuwarsu dangane da dan kwallon kafar.

   Tsohon dan kwallon kafar na Real Madrid ya tafi Portugal ne a ranar Litinin domin ya duba mahaifayarsa da ke asibiti tana karbar magunguna saboda rashin lafiya da take fama da shi.
  A lokacin da ya ke kasar ta Portugal ne aka gano cewar dan tawagarsu Danieli Rugani ya kamu da cutar hakan yasa aka killace sauran 'yan kwallon kungiyar.

  Danieli Rugani bai buga wasar da Juventus da buga da Inter Milan ba yana benci amma daga baya ya shiga dakin canja kaya ya taya 'yan kungiyarsa murna.
  Ronaldo ya tafo Madeira tare da iyalansa kwana guda bayan labarin cewa Rugani yana dauke da cutar ta bi gari.

  Sai dai rahoton da ya fito yanzu ya nuna cewa Ronaldo da iyalansa ba su dauke da kwayar cutar da Coronavirus.
  "Ba zan iya bayar da cikakken bayani ba saboda dalilan tsaro, amma ina son in bayyana cewa an yi nazarin lamarin kuma a halin yanzu babu yiwuar yana dauke da kwayar cutar," kamar yaddda ya yi wa Daily Mail bayani.
  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Yanzu-yanzu: Cristiano Ronaldo baya dauke da Coronavirus Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI