--
"Yan bindiga sun sace Ango da abokanansa guda biyar a jihar Taraba

"Yan bindiga sun sace Ango da abokanansa guda biyar a jihar Taraba

Wasu da ake tunanin 'yan bindiga ne sun sace Ango da abokanansa guda biyar akan hanyar Wukari-Ibi dake jihar Taraba a jiya Juma'a da yamma, mutanen yankin sun sanarwa da Premium Times Mutanen da lamarin ya shafa dai suna kan hanyarsu ta dawowa daga wajen daurin auren ne a Gboko, cikin jihar Benue,

kwatsam sai gani suka yi an dakatar da motarsu a kauyen Dan-Wanzam. Wani babba a yankin da ya nemi a boye sunanshi shine ya bayyana hakan. "Yan bindigar sun tsayar da motar wacce take dauke da angon da abokanansa wadanda suke duka matasa ne. "Hadda angon 'yan bindigar sun sace mutane shida, kuma lamarin ya faru ne kilomita biyar daga garin Ibi. "Yawancin masu garkuwa da mutanen fulani ne da suke zaune a yankin, mun san su duka. Sun bukaci a basu naira miliyan a matsayin kudin fansa wanda muka ki yadda.

"Yan kungiyar sa kai namu suna neman taimako wajen tarar wadannan 'yan bindigar. Gwamnati na bukatar ta tattaro duka 'yan kungiyar sa kai din ta taimaka musu da kayan aiki," cewar mutumin. A yanzu haka dai matasa da sauran mutane na yankin sun hada kai zasu fuskanci 'yan bindigar domin ayi ta ta kare. "Zamu fuskance su saboda yanzu yankin Ibi-Wukari ya zama abin tsoro,

a kowanne lokaci suna iya kaiwa mutane hari. Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, David Misal, ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce wasu da ake tunanin 'yan bindiga ne dauke da bindigu masu kirar AK-47 sun tare hanyar Wukari-Ibi, suka tare wata mota suka shiga daji da mutanen da suke ciki. Ya ce yanzu haka jami'an 'yan sanda sun bazama neman 'yan bindigar domin ceto mutanen da suka sace din.
LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to ""Yan bindiga sun sace Ango da abokanansa guda biyar a jihar Taraba "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?