--
UAE ta tura jirage biyu da kayan agajin coronavirus zuwa Iran

UAE ta tura jirage biyu da kayan agajin coronavirus zuwa Iran

Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta tura jirage biyu dankare da safar hannu da takunkumin rufe baki da hanci da kuma suaran kayan aikin lafiya zuwa Iran, don taimaka wa wurin kawar da cutar Coronavirus.
A yanzu Iran ce kasar da ta fi fuskantar bala'in cutar Covid-19 a duniya, inda mutun 14,000 suka kamu kuma tuni 850 sun mutu.
Dama Iran ta yi kira ga kasashen da ba sa ga maciji da ka da su bari siyasa ta hana su gudanar da aikin agaji.
Tun farko dai sauran kasashen Larabawa kamar Saudiyya sun zargi Iran din da baza coronavirus a fadin duniya ta hanyar barin 'yan kasar ta Saudiyya shiga Iran ba tare da an rattaba wa fasfo dinsu hannu ba.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "UAE ta tura jirage biyu da kayan agajin coronavirus zuwa Iran"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?