--
Tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare – Aliko Dangote

Tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare – Aliko Dangote

Fitaccen attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa gwamnatocin Najeriya na baya da na yanzu basa tabuka wani abin a zo gani wajen ciyar da tattalin arzikin Najeriya gaba, hakan yasa tattalin arzikin baya cigaba. Dangote ya bayyana haka ne yayin wani taro da gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele ya shirya a babban birnin tarayya Abuja, inda yace kokarin da gwamnatin Buhari ken a karkatar da akalar tattalin arzikin Najeriya daga man fetir ya yi kadan.

Dangote ya ce babu wasu takamaimen kwararan tsare tsare da gwamnatin ta tanadar na karkatar da tattalin arzikin kasar daga man fetir, don haka ya bada shawarar akwai bukatar kara kaimi wajen wannan aiki mai muhimmanci, musamman a yanzu da farashin mai ya yi rugu rugu. “Na yi kukar zuci kwarai da gaske lokacin da karanta cewa wai hukumar kwastam ta tara naira tiriliyan 1.35 a shekarar data gabata, hakan ya nuna cewa tattalin arzikin Najeriya baya aiki, saboda idan da yana aiki kamata ya yi a ce hukumar tattara haraji ta kasa, FIRS, ce za ta amshi wadannan kudade.” Inji shi. 

Attajirin ya shawarci gwamnatin Buhari ta kara kaimi wajen bayar da muhimmanci tare da mayar da hankali ga harkar noma da bangaren masana’antu, saboda su ne suke samar da ayyukan yi ga jama’a da dama, kuma suke taimaka ma yan magidanta da iyalansu. Haka zalika Dangote ya bayyana damuwarsa ga hanyoyin da suke Najeriya, musamman wadanda suke kaiwa ga tashoshin jiragen ruwa inda ake shigo da manyan injinonin masana’antu, wanda yace hanyoyin kadai suna tsawwala kudaden da ake kashewa wajen kasuwanci a Najeriya. “A shekarar da ta gabata, 

kamfanoninmu guda 3 kadai sun yi asarar naira biliyan 30 a kan hanyar zuwa tashar Apapa, wanda hakan na nufin ba zamu biya gwamnati harajin da ya kamata ba kenan, don haka akwai bukatar duba maganan hanyoyi da wutar lantarki saboda sune matakalar cigaban matsakaita da kananan masana’antu.” Inji shi. 


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare – Aliko Dangote "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?