--
Haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ta ke yi a Jami'o'i – Inji Chris Ngige

Haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ta ke yi a Jami'o'i – Inji Chris Ngige

Ministan kwadago da samar da ayyukan Najeriya, Dr. Chris Ngige, ya yi magana game da sabanin da gwamnatin tarayya ta samu da kungiyar ASUU ta Malaman Jami’o’i. Dr. Chris Ngige ya bayyana cewa haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ta ke yi a dalilin tursasawa ‘Ya ‘yanta shiga cikin tsarin albashin nan na IPPIS da aka kawo. Dr. Ngige ya yi maganar ne a fadar shugaban kasa bayan an kammala taron FEC a Ranar Laraba. 

Wannan ne karon farko da gwamnati ta yi magana game da yajin kungiyar. Da ya ke amsa tamboyoyin ‘Yan jarida, Ngige ya ce kungiyar ASUU ba ta sanar da gwamnatin tarayya halin da ta ke ciki ba, sai kurum ta tafi yajin aikin makonnni biyu. A cewar Ministan kwadagon, ya na daga cikin rashin gaskiya ace an biya masu yajin aiki albashi domin kuwa ba su yi gumin komai ba a lokacin da su ka kauracewa ofisoshinsu.

ASUU sun fara yajin aiki a Najeriya a kan batun shiga tsarin IPPIS Source: Facebook Ministan kasar ya bayyanawa Manema labarai cewa Ma’aikatarsa ta shirya zama da ‘Yan ASUU a Ranar Alhamis domin shawo kan sabanin da ya shiga tsakaninsu da gwamnati. Ngige ya nuna cewa an jima kadan kungiyar ASUU za ta zauna da shi da Ministan ilmi, da Ministar kudi da tattali da kuma babban akantan Najeriya domin samun mafita. Ko da Ministan ya na sa ran cewa gwamnatin Najeriya za ta shawo kan wannan yajin aiki, 

sai dai ya ce babu ma’aikacin da ya isa ya fadawa gwamnati yadda za a biyasa albashi. Mai girma Ministan ya na ganin yajin aikin da ASUU ta shiga bai halatta ba. Gwamnati dai ta dakatar da biyan albashin wadanda su ka guji IPPIS ne saboda rage facakar kudi. 


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ta ke yi a Jami'o'i – Inji Chris Ngige "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?