--
Sheikh Alzakzaky A Kurkukun Kaduna: Kula da Lafiyar Jagoran 'Yan uwa Musulmi a gidan Yarin Kaduna,Rijiya Ta Bada Amma Guga ya Hana.

Sheikh Alzakzaky A Kurkukun Kaduna: Kula da Lafiyar Jagoran 'Yan uwa Musulmi a gidan Yarin Kaduna,Rijiya Ta Bada Amma Guga ya Hana.


Babban dan Shaikh Alzakzaky,Mohammed Zakzaky, ya koka kan yadda Hukumar gidan Yarin Kaduna ke kawo wasa, cikas da kuma tasgaro a karo na biyu kan barin Likitocin Mahaifinsa su samu cikakkiyar Kulawa da shi da mai dakinsa Zeenatu yadda ya kamata,Kamar yadda Kotu ta yi umurni a kwanakin baya biyo bayan korafin hakan da Lauyoyin Malamin suka gabatar a gaban Kotu kuma kotun ta amince da korafin,tare da umurni a rika bari likitoci na dubasu duk sadda suke bukata.
Ga Hukimar gidan Yarin ta kar6i umurnin da hannun dama amma kuma ta ki binsa da hannun hagu,kamar yadda Mohammed Alzakzaky ke koken haka a wani rubutu da ya saki a yau 13 ga maris,2020.Ga dai abin da yake cewa,kamar yadda wakilinmu ya ci karo da shi:

"Halin Da Mahaifana Suke Ciki A Yanzu."
"Yau dai zan yi Magana akan dokar da ba rubutacciya ba, amma kuma ake aiwatar da ita wajen cutar da mahaifana; a tsammanina shirun da na yi zai taimaka wajen rage irin ukubar da mahaifana suke fuskanta.
Tun mahaifana na tsare a wajen DSS, kafin a mayar da su gidan kurkukun jihar Kaduna; mahaifina na fama da hawan jini sosai, wata rana jininshi ya hau, wata rana ya sauka.Kullum dai haka yake fama da jiki, ban da sauran nau’ikan rashin lafiya da yake fama da.

Mahaifiyata kuwa, bayan dukkan matsaloli na rashin lafiya da take fama da su, a yanzu haka jini ne yake zuba ta bakinta da hanci; saboda dama ta na fama da wani ciwo mai suna "Sinus", wanda ko kadan ba a ta6a yi mata magani ba a cikin shekaru biyar din da suka wuce.
A karshen watan Disamba an ba wasu likitoci damar ganinsu, wadannan likitocin sun bukaci a yi wasu gwaje-gwaje; daga cikin gwaje-gwajen akwai wadanda dole sai an fita da su zuwa asibiti, amma shugabannin gidan yarin suka hana; a cewarsu sai kotu ta amince da hakan.

A ranar 24 ga watan Fabrairu, kotu ta basu umarnin da su bari ayi musu duk abin da ya dace na magani, a ranar 26 likitocin sun sake bukatar ayi wadannan gwaje-gwajen kamar yadda suka bukata a baya; inda muka yi iya kokarinmu don ganin hakan ya faru.
Bayan makonni na shirye-shirye, alkawura don ganin likita da ma asibiti; da ma wasu shirye-shirye da muka yi da shugaban gidan yari na jihar Kaduna, hakarmu ta kasa cimma ruwa, saboda shugabannin gidan yarin sun sake kawo mana cikas kamar yadda suka yi a baya.

Daya daga cikin likitocin mahaifana, wanda shine zai yi gwaje-gwajen; dama kuma shi kadai ne aka bari ya dinga duba mahaifana, ya shaida mana cewa shugabannin gidan yarin sun bukaci da shi da sauran likitocin su rubuta bukata a rubuce, wacce a cewarsu za a kai Abuja domin neman amincewa daga sama.
Don haka a cewarsu dole ne mu zauna da babban likitan gidan yarin jihar Kaduna, da kuma likitan da yake wakiltar jihar Kaduna; a duk sadda suke da lokacin mu zauna da su din. Daga nan sai mu sake bin matakan da muka dauka a tsawon makonni uku, don sake sanya lokacin da za a gudanar da gwaje-gwajen a lokacin da yai musu.

Sannan sun shaidawa likitan cewa ba a yarda a gudanar da wadannan shirye-shiryen tare da wani lauya ba. Mu'azu Dan Musa wanda shine shugaban gidan yarin jihar Kaduna, ya bayyana cewa muddin aka yi kokarin sanya lauya a dukkan shirye-shiryen; to kamar anyi aikin banza ne, don kuwa a cewarshi in aka yi hakan komai ya rushe kenan. Wato ma’ana ba za su sake bari likitoci su duba mahaifana ba.

 Mohammed Ibraheem Zakzaky.
13/03/2020.
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Sheikh Alzakzaky A Kurkukun Kaduna: Kula da Lafiyar Jagoran 'Yan uwa Musulmi a gidan Yarin Kaduna,Rijiya Ta Bada Amma Guga ya Hana."

Post a Comment

Tell us what you think about this article?