--
Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantun kasar kan Coronavirus

Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantun kasar kan Coronavirus

A cikin matakan da take dauke wajen takaita yaduwar cutar Coronavirus, Kasar Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantu da jami'o'in:

masarautar fari daga ranar Litinin har ila ma sha'a llahu. Kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya SPA ta sanar da cewa ma'aikatar Ilimin kasar ta sanar da hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Febrairu 2020. 


Jawabin yace: "An yanke shawarar kulle dukkan makarantu ne saboda kyakkyawar soyayyar da shugabancin ke yiwa yaranta kan tsaronsu kuma za'a samar da wasu hanyoyin ilmantar da su daga gidajensu." 

Ministan harkokin ilimin Saudiyya ya bada umurnin ilmantar da yara daga gidajensu ta hanyar na'urorin zamani. Kawo yanzu, mutane 11 sun kamu da cutar a kasar ta Saudiyya. 


A ranar 5 ga Maris, Shugabancin Masallacin Harami karkashin jagorancin babban limami, Sheikh Abdur-Rahman As-Sudais ta kaddamar da feshi da tsaftace Mataaf na musamman domin kawar da yaduwar cutar Corona. Mabiya addinin Islama a fadin duniya sun yi mamakin hakan inda da dama suka ce wannan shine karo na farko da zasu ga Masallacin Harami babu kowa

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin kasar Saudiyya ta dakatad da aikin Umrah da ziyarar Masallacin Annabi mai girma ga dukkan yan kasar da mazauna sakamakon bullar cutar Coronavirus a kasar. Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta dau matakin ne domin takaita yaduwar cutar a kasar mai alfarma. Gwamnatin kasar Saudiyya ta alanta cewa a mayarwa dukkan wadanda suka biya kudin Umrah kudadensu. 



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Saudiyya ta bada umurnin kulle dukkan makarantun kasar kan Coronavirus "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?