--
Sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shiga gidan sarauta

Sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shiga gidan sarauta



- Sabon Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya koma gidan sarauta a daren ranar Laraba, 11 ga watan Maris - Bayero ya shiga Soron Shekara sannan daga nan ya shiga Soron Ingila, wanda nan ne gidansa a cikin masarautar inda ya ke karban gaisuwa daga ahlin gidan sarauta da sauran sarakunan gargajiya 


- Za kuma a gudanar da hawan daba na musamman domin karrama sarkin, tare da addu’o’i na musamman don zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya koma gidan sarauta a daren ranar Laraba, 11 ga watan Maris, yan sa’o’i kadan bayan ya karbi takardar kama aiki daga wajen gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje. 


Daruruwan al’umman Kano sun isa gidan sarautar domin shaida al’ada na shigar sarki gidan sarautar ta wata kofar tarihi, wacce ta ke al’ada da ke tabbatar da daura Bayero a matsayin sarki.


Sabon sarkin wanda ya kasance mai digiri a fannin sadarwa daga jami’ar Bayero, kuma kwararren matukin jirgi, Aminu Ado Bayero ya shafe mafi akasarin rayuwarsa yana yiwa masarautar Kano hidima. Ya riki mukamai daban-daban da suka hada da Turaki, Sarkin Dawakin Tsakar Gida, da kuma Wambai na Kano. Ya kuma kasance sarkin Bichi kafin a nada sa a matsayin sarkin Kano a yanzu. A kwanaki masu zuwa, Bayero zai ci gaba da aiwatar da wasu al’adu da suka hada da jagorantar zaman majalisar sarakunan gargajiya na Kano.


Za kuma a gudanar da hawan daba na musamman domin karrama sarkin, tare da addu’o’i na musamman don zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya shiga gidan sarauta"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?