MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"

Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Sunday, March 8, 2020

  Naira Marley ya yi magana bayan Budurwa ta fito da bidiyonsa a dakin Dubai

  Wata Baiwar Allah mai matsakaicin shekaru ta fito da wani bidiyo inda aka ga fitaccen Mawakin nan Naira Marley a kan gado ya na barci. Wannan Budurwa ta yi ikirarin cewa ta dauki bidiyon ne bayan sun gama holewarsu tare da Mawakin a wani otel a kasar Larabawa. Idan bidiyon ya tabbata na gaske, 
  an yi wannan danyen aiki ne a Birnin Dubai da ke kasar UAE a Yankin Gabashin Nahiyar Asiya a Duniya. Wannan Mata da sunan ta bai bayyana mana ba tukun, ta bayyana cewa sun kwana da Mawakin ne a katafaren otel dinnan na Burj Al Arab. Burj Al Arab ya yi suna a Duniya inda jama’a su ka saba zuwa domin su huta. Kudin kwanan daki a otel ya kai N500, 000 a kudin Najeriya.   An wallafa wannan bidiyo a shafin Instablog na Instagram. Fiye da mutane 500, 000 su ka kalli wannan faifai a wannan dandalin na zumunta. A bidiyon an ga wannan Budurwa ta nuna fuskarta cikin farin ciki. Ba dai wannan ba ne karon farko da Naira Marley ya jawo abin magana. 


  Asalin sunan Mawakin Azeez Fashola, kuma shi ne shugaban gungun wasu Matasan zamani da su ke kiran kansu Marlians yanzu a Najeriya. Bayan wannan bidiyo ya fito, Matashin Mawakin ya fito gaban Duniya ya bayyana cewa bai ji kunyar komai ba, domin dama can bai da kunya.

  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Naira Marley ya yi magana bayan Budurwa ta fito da bidiyonsa a dakin Dubai Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI