Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com "Colour"
 • LABARAN YAU

  Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki,

  ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________
  Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views

  Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: zaidusuleiman47@gmail.com

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Wednesday, March 25, 2020

  Masu dauke da coronavirus yanzu a Najeriya sun kai 46 yayinda NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 2  - Yanzu mutane da ke dauke da coronavirus a Najeriya sun kai 46 bayan an sake samun sabbin mutane biyu
  - Cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya ce ta sanar da hakan a safiyar yau, Laraba, 25 ga watan Maris

  - An samu mutum guda a jahar Osun yayinda dayan ke a jahar Lagas Cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa an samu Karin mutane biyu da ke dauke da cutar coronavirus a Najeriya. Hukumar NCDC ta shafinta na Twitter a ranar Talata, 24 ga watan Maris, ta bayyana mutum guda a Osun yayinda dayan ya ke a jahar Lagas.

  Ta wallafa: “An tabbatar da sabbin lamuran #COVID19 a Najeriya: 1 a Lagas sannan 1 a Osun. “Dukaninsu sun kasance matafiya da suka dawo Najeriya cikin kwanaki 7 da suka gabata.

  “Da misalin karfe 07:00 na safiyar ranar 25 ga watan Maris, an tabbatar da masu dauke da #COVID19 46 a Najeriya. An sallami mutane 2 sannan mutum 1 ya mutu.” A bangare guda mun ji cewa Bala Mohammed, gwamnan jihar Bauchi, ya bukaci jama'ar jiharsa da kada su ji tsoro a kan kebancesa da aka yi sakamakon cutar coronavirus da ya kamu da ita. A ranar Talata ne dai aka tabbatar da cewa gwamnan na dauke da cutar coronavirus din. Mohammed ya killace kansa tun bayan da yayi hannu da dan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, wanda aka gano yana dauke da cutar, kamar yadda jaridar The Cable ta wallafa.

  A sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na twitter, Mohammed ya ce yana lafiya kuma har yanzu bai fara nuna wata alama ta cutar ba. "Kamar yadda zai yuwu kun sani, an gano ina dauke da coronavirus," Mohammed yace. "Tuni na killace kaina na kwanakin da suka gabata kuma har yanzu ina kebance har sai na samu tabbaci daga likitoci cewa zan iya ci gaba da mu'amala da jama'a. Ina lafiya kuma ban fara nuna wata alamar cutar ba. Ina kira ga kowa da ya kwantar da hankali kuma kada a firgita. Za mu tsallake." yace.


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Masu dauke da coronavirus yanzu a Najeriya sun kai 46 yayinda NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 2 Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI