--
Kano: Sabon sarki ya garzaya gaban mahaifiyarsa don neman tabarraki

Kano: Sabon sarki ya garzaya gaban mahaifiyarsa don neman tabarraki


- A yau Talata ne sabon Sarkin Kano, Aminu Bayero ya ziyarci makabartar da sarakunan Kano ke kwance a gidan sarki da ke Nassarawa - Aminu Bayero ya ziyarci makabartar da sarakunan Kano ke kwance ne don yin adu’o’i ga mahaifinsa marigayi Alhaji Ado Bayero 

- Sabon Sarkin ya kara da garzayawa zuwa wajen mahaifiyarsa da ke unguwar Gandun Albasa domin neman tabaraki garesa da sauran hakiman Kano A yau Talata ne sabon Sarkin Kano, Aminu Bayero ya ziyarci makabartar da sarakunan Kano ke kwance a gidan sarki da ke Nassarawa don yin adu’o’i ga mahaifinsa marigayi Alhaji Ado Bayero. 

Sabon Sarkin ya kara da garzayawa zuwa wajen mahaifiyarsa da ke unguwar Gandun Albasa domin neman tabaraki garesa da sauran hakiman Kano da suka yi mubaya’a.

Ya kara da biyowa ta titin gidan Zoo daga nan ya wuce gidansa da ke Mandawari duk a cikin birnin Kanon. Kamar yadda gidan rediyon Freedom da ke Kano ta ruwaito, jama’ar jihar Kano da kuma jami’an tsaro ne suka raka sabon sarkin wajen mahaifiyarsa

Amma kuma, A yau Litinin 10 ga watan Maris ne al'ummar Kano da dama suka yi tururuwa zuwa gidan sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero domin taya shi murnar nadin da aka masa a matsayin sarki. Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya nada Aminu Ado Bayero ne bayan ya cire tsohon sarki Muhammadu Sanusi II a kan dalilan rashin yi wa gwamnati da'a. 


Mutanen sun isa gidan suna kirari da wakoki na murnar nada sabon sarki a Kano. Daga bisani, sabon Sarki Aminu Ado Bayero ya ziyarci ya fito daga gida ya tafi gidan Nasarawa inda kaburburan kakakansa da mahaifinsa su ke.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Kano: Sabon sarki ya garzaya gaban mahaifiyarsa don neman tabarraki "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?