--
Coronavirus: Gwamnatin Iran Ta Ware Dala Biliyan 5 Don Tallafa Wa 'Yan Kasuwan Da Coronavirus Ta Cutar

Coronavirus: Gwamnatin Iran Ta Ware Dala Biliyan 5 Don Tallafa Wa 'Yan Kasuwan Da Coronavirus Ta Cutar

A kokarin gwamnatin Iran na rage wa al'ummar kasar hasarar da suka fuskanta sakamakon bullar annobar Coronavirus a kasar, babban bankin ya sanar da ware kudaden da suka Dalar Amurka biliyan 5 don ba wa ‘yan  kasuwa da masu masu masana'antu da suka cutu sakamakon bullar annobar Coronavirus a kasar a matsayin bashi da nufin farfado da wadannan harkoki na su na kasuwanci.

Gwamnan babban bakin na Iran Abdulnasir Himmati ne ya bayyana inda ya ce nan ba da jimawa ba za a fara raba bashin ga ‘yan kasuwan da abin ya shafa wadanda kuma suke bukata don farfado da harkokin kasuwancin na su da suka cutu sakamakon bullar annobar.

Gwamnan babban bankin ya ce an dau wannan matsayar ne bayan taron majalisar ministoci karkashin jagorancin shugaban kasa Dakta Hasan Rouhani don tattauna yadda za a bullo wa cutar ta Covid-19 musamman a bangaren magance hasarori a bangaren tattalin arziki da aka fuskanta.

Wannnan dai yana daga cikin shirin da gwamnatin ta Iran ta bullo da shi ne da nufin rage radadin rashin da al'ummar kasar suka fuskanta musamman wadanda suka rasa  ayyukansu ko kuma wadanda jarinsu ya karye sakamakon bullar annobar Coronavirus din a kasar wacce take ci gaba da shafan bangarori daban-daban na tattalin arzikin duniya.

Kafin hakan ma dai gwamnatin ta Iran ta fara aiwatar da wani shiri na tallafa wa marasa karfi a kasar da wasu kudade don su yi amfani da su wajen tafiyar da rayuwarsu sakamakon killace al'umma da tilasta musu zaman gida da aka yi don hana yaduwar cutar.

Tuni dai aka fara zuba wadannan kudade na tallafi cikin asusun banki na iyalan da suke bukatar taimakon.

Kasar Iran dai tana daga cikin kasashen da annobar Coronavirus din ta yi wa barna sosai inda sama da mutane 2300 suka rasa rayukansu tun bayan bullar cutar a kasar.
LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Coronavirus: Gwamnatin Iran Ta Ware Dala Biliyan 5 Don Tallafa Wa 'Yan Kasuwan Da Coronavirus Ta Cutar"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?