LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya kamu da coronavirusGwamnan iihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce ya kamu da cutar coronavirus.
Gwamnan ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi ranar Asabar, inda ya ce ya killace kansa.

Kazalika ya ce har yanzu bai fara nuna alamun cutar ba.
"A farkon makon nan ne na yi gwajin cutar Covid-19, kuma sakamakon ya fito a yammacin yau. Ina mai bakin cikin shaida muku cewa ina dauke da cutar," in ji El-Rufai a wani bidiyo da gwamantin Kaduna ta wallafa a Twitter.

"Kamar yadda hukumomin lafiya suka tsara kan abin da mai dauke da cutar ya kamata ya yi, na killace kaina. Mataimakin gwamna zai ci gaba da jan ragamar kwamitin musamman kan Covid-19 sannan zan ci gaba da bayar da bayanai lokaci zuwa lokaci."
Nasir El-Rufai ya yi kira ga al'ummar jihar Kaduna su ci gaba da bin dokar da gwamnatinsa ta kafa a jihar da kuma shawarwarin hukumomi domin kare kansu daga Covid-19.Social KADUNA UPDATE: Malam Nasir @elrufai has disclosed that he has tested positive for Covid-19. He is in self-isolation as required by the case management guidelines of the NCDC for a someone that is not showing symptoms. pic.twitter.com/5lqfvWc4zv

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YKU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
b

Post a comment

0 Comments