--
Ganduje ya bukaci Sarki Muhammadu Sunusi ya nada sabbin hakimai

Ganduje ya bukaci Sarki Muhammadu Sunusi ya nada sabbin hakimai




Gwamnatin jahar Kano a karkashin umarnin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ce ta bukaci mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya gaggauta nada wasu manyan fadawarsa mukamin hakimai a karkashin masarautarsa.

Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya umarci Sarki Sunusi ya nada manyan fadawansa da suka hada da masu zaben Sarkin Kano domin su jagoranci wasu kananan hukumomi na daban dake karkashin ikon Sarkin.

Gwamnatin ta umarcin Sarkin ne cikin wata wasika dake dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jahar Kano, Alhaji Usman Alhaji, mai dauke da kwanar wata 2 ga watan Maris na shekarar 2020.

Wasikar ta ambaci sunayen manyan fadawan Sarkin da gwamnati take bukatar ya nadasu hakimai akwai Alhaji Mukhtar Adnan, Alhaji Yusuf Nabahani Ibrahim Cigari, Alhaji Abdullahi Ibrahim da Alhaji Abubakar Bello Tuta.

“Biyo bayan kirkirar sabbin masarautu a jahar Kano, a yanzu masu zaben sarkin Kano suna karkshin masarautar Kano, don haka ake kira ga mai martaba Sarkin Kano ya gaggauta shirin nada wadannan masu zaben Sarki mukamin hakimai a kananan hukumomin dake karkashin ikonsa.

“Kamar yadda doka ta tanada, ana bukatar mai martaba Sarki ya tura masu zaben Sarkin zuwa kananan hukumomin da suka kamata bayan samun amincewar mai girma gwamnan jahar Kano, muna kira ga Allah Ya shiryi Sarki.” Inji wasikar.

A wani labarin kuma, shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Kwamared Adams Oshiomole ya bayyana dalilin da yasa wasu yayan jam’iyyar APC wadanda yake kallonsu a matsayin makiyansa suke kokarin tsige shi daga kujerar shugabancin jam’iyyar.


Oshiomole ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin Najeriya a ranar Alhamis.

Oshimole ya bayyana cewa duk masu son ganin bayansa a jam’iyyar APC suna yi ne kawai don suna son zama shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2023, amma kuma basu da iko da jam’iyyar a jahohinsu.

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Ganduje ya bukaci Sarki Muhammadu Sunusi ya nada sabbin hakimai"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?