--
COVID-19: Sabbin mutum 11 sun kamu a Najeriya, jimilla 81

COVID-19: Sabbin mutum 11 sun kamu a Najeriya, jimilla 81



Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya (NCDC) ta kara tabbatar da sabbin mutane 11 da suka kamu ta kwayar cutar Covid-19 wato coronavirus a kasar. An samu karuwar mutane takwas ne a Legas sannan guda biyu a Enugu sai kuma daya a jihar Edo. Hakkan na nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar a kasar a halin yanzu ya kai 81.


A cewar hukumar ta NCDC, "an samu sabbin mutane 11 da suka kamu da Covid-19 a Najeriya; 8 a jihar Legas, 2 a Enugu da kuma guda daya a jihar Edo kawo yanzu a ranar 27 ga watan Maris na 2020 misalin karfe 11.55 na dare, jimlar wanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar 81. An sallami mutane 3 sai kuma mutum daya ya mutu."


Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane fiye da 15,000 a fadin duniya. Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, sannan an sallami mutane biyu da suka warke bayan sun sha magungun a cibiyar da aka killace su, kamar yadda kididdigar NCDC ta nuna. Yawacin mutanen da aka samu da kwayar cutar corona a Najeriya,
'yan kasa ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai. An tabbatar da samun kwayar cutar a jikin manyan jami'an gwamnati guda uku ciki har da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin shugaban kasa Abba Kyari da a halin yanzu yana samun kulawa daga likitoci.

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "COVID-19: Sabbin mutum 11 sun kamu a Najeriya, jimilla 81 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?