MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Thursday, March 26, 2020

  COVID-19: Buhari ba ya tari bayan gwaji, mu na zargin ma'aikatan Aso Rock 4,370 - Fadar shugaban kasa
  Gwamnatin tarayya ta ce tana kan tsamo mutanen da ake zargi da mu'amala da wadannda cutar COVID-19 ta kama. A halin yanzu kuwa ta tsamo mutane har 4,370. 


  Ta bayyana damuwarta da yadda da yawan wadanda suka dawo daga kasashen ketare suka bada adireshin bogi. Gwamnatin tarayyar ta kara da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya tari kuma an tabbatar da cewa baya dauke da muguwar cutar Coronavirus.   Shugaban kasar na nan lafiya kalau kuma cikin koshin lafiya. Ministan yada labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ya sanar da hakan yayin bayani a game da cutar COVID-19. 


  Ya ce: "A halin yanzu mun zakulo mutane har 4,370 kuma muna rokon duk wanda yayi wata mu'amala da wadanda ke dauke da cutar ya garzaya ya kai kansa hukumomin da suka dace. 


  Muna kira ga 'yan Najeriya da su goyi bayan hukumomin." "Muna gab da bayyanar da cutar a tsakaninmu, don haka dole ne mu hana hakan ko kuma mu fuskanci kalubale mai yawa a kwanaki kadan masu zuwa. Babu wata hanya ne sai hakan." Ministan ya ce gwamnati ta damu matuka ta yadda wasu masu dawowa daga kasashen ketare suka bada adireshin bogi.   "Babu boye-boye, zan iya cewa bama samun hadin kan da muke bukata a halin yanzu daga 'yan Najeriya. Wasu na nan suna caccakar gwamnati a maimakon hada kai da ita tare da bin ka'idojin hana yaduwar cutar.


  "Wasu 'yan Najeriya da suka shigo kasar nan daga kasashen ketare sun bada adireshin bogi da lambar wayar karya. Hakan yasa muke fuskantar tsananin wahala wajen nemo su a lokacin da bukatar hakan ta taso. 


  "Wasu 'yan Najeeriya kuwa sun ki bin dokar rashin shiga jama'a masu yawa, yayin da wasu malaman addini suka ki bin dokar kasar. "Gwamnati na yin duk abinda za ta iya amma muna bukatar hadin kan 'yan kasa. Mun wuce matakin roko da bayani, yanzu lokacin yin tilas ne." A bangaren koshin lafiyar shugaban kasa Buhari,   Ministan ya ce "Shugaban kasa na lafiya kuma cike da koshin lafiya. Hakazalika yana ci gaba da mulki. Wasu na zargin cewa shugaban kasar yana tari, wannan karya ne kuma labaran kanzon kurege ne marasa tushe da makama." LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: COVID-19: Buhari ba ya tari bayan gwaji, mu na zargin ma'aikatan Aso Rock 4,370 - Fadar shugaban kasa Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI