--
Coronavirus: Gwamnatin Kano ta hana manyan motocin daukar fasinjoji shiga jahar

Coronavirus: Gwamnatin Kano ta hana manyan motocin daukar fasinjoji shiga jahar



- Gwamnatin Kano ta bayar da umarnin dakatar da manyan motoci da ke daukar fasinjoji masu zuwa Kano daga Legas shiga jahar - Hakan na daga cikin yunkurin hana yaduwar cutar coronavirus a jahar

- Gwamnatin ta ce ta haramta wa motocin shiga jahar sakamakon motocin na daukar mutane masu dimbim yawa wanda hakan zai iya sa wa a samu bullar cutar Gwamnatin jahar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ta bayar da umarnin dakatar da manyan motoci da ke daukar fasinjoji masu zuwa Kano daga jahar Legas shiga jahar. Hakan na daga cikin yunkurin hana yaduwar cutar coronavirus da gwamnatin Kano ke yi.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta haramta wa motocin kirar Luxurious shiga jahar sakamakon motocin na daukar mutane masu dimbim yawa wanda hakan zai iya sa wa a samu bullar cutar.

A bangare guda mun ji cewa Majalisar Malamai da Limaman jihar Kaduna sun bukaci dakatad da Sallar Juma'a da Khamsu-Salawati idan mamu sun zarce mutane 20 a fadin jihar saboda annobar COVID-19. Sakatare Janar na majalisar, Malam Yusuf Arrigasiyyu, a jawabin da ya sake ranar Talata a Kaduna, ya shawarci dukkan Masallatan Juma'a su dakatar. A cewarsa “Muna bada shawaran cewa dukkan Masallatan Juma'a da Khamsu-Salawati da adadin mamu ya zarce 20 su dakatar har sai lokacin da aka sanar a bude.“

“Majalisar ta jaddada cewa sun dau wannan mataki ne bisa ga koyarwan Manzon Allah (SAW).“ “Hakazalika muna kira ga mutan jihar Kaduna su bi umurnin likitoci a koda yaushe kuma su guji yada cutar coronavirus.“ Arrigasiyu ya jinjinawa gwamnatin jihar Kaduna kan matakan da ta dauka wajen hana shigowar cutar jihar Kaduna. Majalisar ta yi kira ga mutane su taimakawa makwabtansu da wannan kulle zai shafa musamman bangaren kayan abinci da rayuwar yau da kullum. Ya bukaci yan uwa Musulmai su kasance cikin addua da kai dauki wajen Allah don kawar mana da wannan cutar.

LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Coronavirus: Gwamnatin Kano ta hana manyan motocin daukar fasinjoji shiga jahar "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?