--
Coronavirus: Bayan watanni biyu da bullarta a Sin, ta ratsa kasashen duniya 66 (Kalli jerinsu)

Coronavirus: Bayan watanni biyu da bullarta a Sin, ta ratsa kasashen duniya 66 (Kalli jerinsu)



Akalla mutane 3000 sun mutu kawo yanzu a sakamakon cutar coronavirus da ta barke a kasar Sin. Wannan cuta ta fito ne a Yankin Wuhan, kafin cutar ta fara zagaya Duniya. Kawo yanzu kimanin mutane 80,000 suka kamu da wannan cuta a fadin kasar Sin da kuma kimanin 4000 a ksar Koruya ta kudu. Bullowar cutar a kasar Koriya ta kudu, inda itace mafi girma bayan Kasar Sin da cutar ta fito. Ga jerin kasashe 66 da cutar ta bulla yanzu: 

1. Afghanistan
 2. Algeria 
3. Australiya 
4. Austria 
5. Azerbaijan
6. Bahrain 
7. Belgium 
8. Brazil 
9. Cambodiya 
10. Sin 
11. Czech 
12. Canada 
13. Croatia 
14. Denmark 
15. Dominica 
16. Ecuador 
17. Misra 
18. Faransa 
19. Geogiya 
20. Jamus 
21. Greece 
22. Hong Kong 
23. Iceland 
24. Indiya 
25. Indonisiya 
26. Iraqi 
27. Iran 
28. Izraila 
29. Italiya 
30. Japan
31. Kuwait 
32. Lebannon 
33. Lithunia 
34. Luxewmborg 
35. Macau 
36. Malayssiya 
37. Mexico 
38. Nepal 
39.Holand 
40. New Zealand 
41. Najeriya 
42. North Macedoniya 
43. Norwway 
44. Oman 
45. Pakistan 
46. Fillibin
47. Tunisiya 
48. Jordan 
49. Qatar 
50. Romaniya 
51. Rasha 
52. San Marino 
53. Singapore 
54. Saudiyya 
55. Koriya ta kudu 
56. Sifen 
57. Sri Lanka 
58. Senegal 
59. Sweden 
60. Switzerland 
61. Taiwan 
62. Thailand 
63. UAE 
64. Birtanniya 
65. Amurka 
66. Vietnam 


A ranar Litinin, 2 ga watan Maris, Kasar Tunisiya da da kasar Senegal sun tabbatar da bullar cutar Coronavirus na farko, hakan ya ya kai adadin kasashen da ta bulla a nahiyar Afrika biyar. Gabanin shigarta kasashen nan biyu a yau Litinin, kasashen Misra, Algeria, da Najeriya sun tabbatar da bullar cutar da ta hallaka akalla mutane 3000 a fadin duniya. 

A wani hira da manema labarai da ministan kiwon lafiyan kasar Senegal, ya shirya a birnin Dakar ranar Litinin, ya bayyana cewa wani dan kasan Faransa ya shigo da cutar kasar. A kasar Tunisiya kuwa, wani dan kasar Italiya ne ya jajubo musu cutar. LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


0 Response to "Coronavirus: Bayan watanni biyu da bullarta a Sin, ta ratsa kasashen duniya 66 (Kalli jerinsu) "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?