MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"

Kusauke Manhajar Bzglobalservice.com.ng Acikin Wayoyinku Na Android Kyauta Domin Samun Labarai

MUNA SIYAR DA DATA TA SHIGA YANAR GIZO TA KAMFANIN MTN DOMIN SIYA DANNA HOTON DAKE QASA YANZU

 • Latest News

  Tuesday, March 10, 2020

  Buri na na karshe a rayuwa shine in mutu a kan kujerar sarautar Kano - Sanusi II

  A jiya Litinin 9 ga watan Maris na 2020 ne gwamnatin jihar Kano ta tsige Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ta katse masa hanzarin cika daya daga cikin burinsa na karshe a rayuwa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Watanni shida da suka wuce, 

  tubabben sarkin a wata hira da ya yi na domin bikin nadin sarautarsa a 2015 ya shaidawa manema labarai a fadar Sarkin Kano cewa burinsa na karshe a rayuwa shine ya mutu a matsayin sarki. A ranar 4 ga watan Fabrairun 2015, Sanusi da ya zama sarki a ranar 8 ga watan Yunin 2014 ya ce, "babu matsayin da ya fi kujerar Sarki."

  Buri na na karshe a rayuwa shine in mutu a kan kujerar sarautar Kano - Sanusi II Source: Twitter 

  Da ya ke magana a kan darajar da ya samu, Sanusi ya ce: "Ba ni da wani matsayi ko kadara. Addu'a ta shine daga fada a kai ni kabari na. Ba ni da wata bukata a rayuwa da ta wuce hakan. Na girma a fada kuma a gani na babu wani abinda ya fi sarkin Kano muhimmanci, kaka na da tsohon sarkin Kano. 

  "Mukami ba komi bane; abinda ke da muhimmanci shine aikin da ka yi. A karshe kowa yana son ya bar tarihi mai kyau. Ina son in yi aikin da al'ummar Kano za su cigaba da min addu'a bayan na mutu saboda jagoranci na gari da na yi. "Babu wani gida da mutum zai so ya zauna da ya fiye fadar nan; Babu wani abu da mutum zai bukata a rayuwa da Allah bai bani ba." 

  Da ya ke amsa tambaya a kan yadda ya ji da masu zaben sarakuna suka zabe shi a matsayin Sarki, Sanusi II da aka haifa a ranar 31 ga watan Yulin 1961 ya ce abu ne mai wahala ya bayyana yadda ya ji. Ya ce yana da matukar wahala mutum ya fadi yadda ya ke ji bayan an nada shi sarki amma ya kara da cewa Al-Kurani bai bar komai ba kuma kalaman da suka fi dacewa ko wane dan sarki ya fadi sune kalaman da Annabi Yusuf (AS) ya fadi bayan Allah ya ba daukaka shi da matsayi.

  Ya ce: "Ya mahaifina, wannan shine abinda na gani a mafarki na; Allah ya kaddara aukuwar abinda na yi mafarki...' 

  idan akwai wani abu da kowane musulmi ya yarda da shi shine Allah kadai ke bayar da mulki kuma Allah ne ya san dalilin da yasa ya zabe shi a wannan lokacin.' LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Buri na na karshe a rayuwa shine in mutu a kan kujerar sarautar Kano - Sanusi II Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI