--
Babu bata lokaci: Tubabben Sarkin Kano ya kammala shirin barin fada, zai bar Kano

Babu bata lokaci: Tubabben Sarkin Kano ya kammala shirin barin fada, zai bar Kano

Tsohon sarkin Kano da gwamnatin ta tube wa rawani a ranar Litinin, Muhammadu Sanusi II, zai bar jihar Kano a yau, Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa cewa masanarta ta tabbatar mata. Kazalika, majiyar ta sanar da Daily Trust cewa tuni gungun jami'an tsaro suka kwace iko da fadar domin fitar da Sanusi daga jihar Kano. 

Sai dai, a wani labarin da Legit.ng ta samu daga shafin jaridar BBC Hausa na nuni da cewa tuni an fitar da Sanusi daga fadar Kano, kuma za a raka shi ya hau jirgi don barin Kano. Kwamishinan yada labaran jihar Kano, Muhammde Garba, ya tabbatar wa da BBC cewa an bawa Sanusi tsaro, a saboda haka ba ya fuskantar wata barazana a yayin da za a raka wurin da zai zame masa mafaka. Wata majiya mai kusanci da fadar Kano ta sanar da Daily Trust cewa Sanusi zai tashi zuwa Abuja a yau, Litinin. 

Rundunar jami'an tsaro a ranar Litinin ta tsinkayi fadar Sarkin Kano da ke jihar Kano. Wannan ya biyo bayan tumbuke Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da ofishin gwamnan jihar yayi. Rundunar jami'an tsaron da suka hada da 'yan sanda da jami'an NSCDC ne suka mamaye harabar fadar, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito. Gwamnati ta jibge jami'an tsaro a fadar ne gabanin sanar da sabon sarkin da zai maye gurbin sarki Sanusi, kamar yadda jawabin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana bayan sanar da tsige Sanusi. 



LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Babu bata lokaci: Tubabben Sarkin Kano ya kammala shirin barin fada, zai bar Kano "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?