MUJALLAR LABARAI, ROHOTANNI, BINCIKE, SHARHI, AL'AJABI, ILMANTARWA FADAKARWA DA NISHADANTARWA "Colour"
 • Latest News

  Latsa Koren Hoton Dake Qasa Domin Sauke Manhajar Labari Awayarka Ta Hannu Kyauta

  Monday, March 9, 2020

  An fitar da Sarki Sanusi na II daga Fadar Kano  Jamai'an tsaro a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun fitar da Sarki Muhammadu Sunusi II daga Fadar Kano, sa'oi bayan da gwamnatin jihar ta sanar da matakin sauke shi daga sarauta.


  Kwamishinan yada labaran jihar Kano Muhammad Garba ya tabbatar wa da BBC batun, inda ya ce sarkin na cikin kariya ba tare da wata muzgunawa ba.
  "Sannan za a kai shi garin da zai zame masa mafaka ya ci gaba da rayuwa a can," a cewar Muhammad Garba.


  Tun da fari dai rahotanni daga Fadar Sarkin Kano sun ce jami'an tsaro sun yi ta harba hayaki mai sa hawaye a fadar sarkin bayan tsige shi.
  Wakilan BBC sun ce jami'an tsaron sun kutsa har cikin gidan sarkin inda mata suke, sai dai matan sun yi ta mayar da martani da jifa da duwatsu.
  Wakilan BBC kusan uku da ke wajen sun tabbatar da cewa sun ga wani baban jami'in gwamnatin Kano ya jagoranci 'yan daba fiye da 50 cikin Fadar Kanon.
  A ranar Litinin ne Sakataren Gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya bayyana dalilan cire sarkin.
  Sanarwar ta ce daukacin mambobin majalisar zartarwar jihar sun amince a cire Sarkin.  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: An fitar da Sarki Sanusi na II daga Fadar Kano Rating: 5 Reviewed By: Admin
  AIKA LABARI