--
Anyi gudun fanfalaki a wajen wani cin abinci bayan wani dan kasar China da ake tunanin yana da Coronavirus yaje wajen

Anyi gudun fanfalaki a wajen wani cin abinci bayan wani dan kasar China da ake tunanin yana da Coronavirus yaje wajen

Masu cin abinci a otel din Naivasha sun ranta ana kare bayan wani dan kasar China ya shiga wajen domin ya sayi abinci A ranar Talatar 11 ga watan Fabrairu, K24 TV ta ruwaito yadda wasu masu cin abinci a wani otel dake Kamere suka ranta ana kare, bayan wani dan kasar China da alamun sa ke nuni da cewa bashi da lafiya ya shiga wajen cin abincin. 

"Dan China din kwarai bashi da lafiya, kuma saboda tsoron cutar Coronavirus ya sanya mutane guduwa daga cikin otel din a lokacin da ya shiga," wani wanda lamarin ya faru a gabanshi ya bayyana. 

Anyi gudun fanfalaki a wajen wani cin abinci bayan wani dan kasar China da ake tunanin yana da Coronavirus yaje wajen Source: Facebook A cewar mutumin, mutanen yankin suna zaune cikin tsoro da fargaba tun lokacin da wannan cuta ta Coronavirus ta kunno kai, inda ya bayyana cewa saboda wajen akwai 'yan China da yawa.

Bayan ma'aikatan lafiya sunje otel din sun tarar da cewa dan China din har ya gama abinda zai yi ya wuce, kuma ma'aikatan otel din basu tambayi ko shi wanene ba. "An sanar da jami'an cewa akwai wani dan China da yaje otel din da bashi da lafiya, bayan zuwansu wajen sun tarar da ya riga ya tafi, kuma babu wanda ya san daga inda ya zo." Cewar ministan lafiya na Nakuru, Cif Samuel King'ori. A yankin Suswa, Narok County kuma, mutanen yankin sun bukaci ma'aikatar lafiya da ta dinga mayar da hankali tana bincikar 'yan kasar China da aka ga cewa ba su da lafiya. 


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y


KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Anyi gudun fanfalaki a wajen wani cin abinci bayan wani dan kasar China da ake tunanin yana da Coronavirus yaje wajen"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?