LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Annobar Corona: Gwamnatin Saudiyya ta umarci Musulmai su dakatar da batun aikin Hajji

Gwamnatin kasar Saudiyya ta nemi musulman duniya da su dakatar da batun zuwa aikin Hajjin bana har sai yadda hali yayi game da annobar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, watau Coronavirus. Kamfanin dillancin labaru na AFP ta bayyana cewa kasar Saudiyya ta dakatar da aikin Umrah tun a farkon shekarar nan sakamakon tsoron da take ji na shigar mata da cutar Coronavirus cikin kasa.

Minista mai kula da aikin Hajji, Mohammed Benten ne ya sanar da haka a ranar Talata, inda yace: “Gwamnatin Saudiyya a shirye take ta hidimta ma bakinta masu zuwa aikin Umrah da Hajji, amma a halin da ake ciki na wannan annobar da ta mamaye duniya.. “Gwamnatin Saudiyya tana lura da lafiyar yan kasar ta da sauran Musulman duniya masu zuwa ibada a kasar, don haka muna shawartar yan uwanmu Musulmai su jinge batun zuwa aikin Hajji har sai an samu saukin annobar nan.” Inji shi.

Wannan annoba ta Coronavirus ta watsu har a kasar Saudiyya, inda ta kama mutane 1,563 sa’annan ta kashe akalla mutane 10, wanda hakan tasa ta kulle masallatanta na kasar gaba daya, tare da hana taron mutane don rage yaduwar cutar.

A wani labari kuma, biyo bayan samun rahotanni dake nuna cewa an samu bullar annobar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus a kurkukun jahar Kaduna, kingiyar yan Shia ta Najeriya, IMN, ta koka kan halin da shugabanta, Ibrahim Zakzaky ya shiga. IMN ta bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunta, Ibrahim Musa wanda yace gwamnatin tarayya za su kama idan wani abu ya samu shugabansu a kurkukun Kaduna.

A cewarsa, aikin gwamnatin tarayya ne ta kare dukkanin mazauna gidan yari, musamman bayan samun bullar cutar Coronavirus a gidan yarin Kaduna, saboda aiki doka cewa ta yi wanda ake zargi ba shi da laifi har sai kotu ta tabbatar masa da laifin.


LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1YKU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 
b

Post a comment

0 Comments