--

An cire dokar hana yara mata masu ciki zuwa makaranta a kasar Sierra-Leone

An cire dokar hana yara mata masu ciki zuwa makaranta a kasar Sierra-Leone

- A ranar Litinin, 30 ga watan Maris ne gwamnatin kasar Sierra Leone ta janye dokar hana yara mata masu juna biyu zuwa makaranta

- Tun a 2015 gwamnatin kasar Sierra Leone ta saka dokar hana yara mata masu juna biyu zuwa makaranta - Amma kuma bayan fafatawa da aka yi da gwamnatin kasar da kungiyar kare hakkin dan Adam a kotu, kungiyar tayi nasara inda aka janye dokar Kasar Sierra Leone a ranar Litinin ta dage dokar hana yara mata masu juna biyu halartar makaranta.

Wannan dokar an dage ta ne a ranar Litinin 30 ga watan Maris bayan fafutukar masu rajin kare hakkin dan Adam wanda ya dauka shekaru biyar. Wannan dokar kuwa an samar da ita ne a shekarar 2015 bayan hauhawar fyade, cin zarafi da talauci yayin barkewar annobar Ebola wacce ta kawo hauhawar ciki ga yara mata masu karancin shekaru.

A yayin da gwamnatin kasar ta jaddada cewa yara mata masu juna biyu ba za su halarci makarantu ba, ta sa ana tsangwamarsu sannan ana kyamarsu a cikin jama'a. A takardar da ke bayyana janye dokar, an bayyana cewa ma'aikatar ilimin firamare da sakandire tana sanar da dage dokar hana yara mata masu juna biyu halartar makarantu. "Janye dokar mataki ce na farko da ke bayyana kokarin gwamnatin kasar Sierra Leone na samar da ingantaccen ilimi ga yara."

Ministan ilimi, David Sengeh ya ci gaba da bayyana cewa dage dokar za a maye gurbinta da sabbin dokoki biyu. Judy Gitau, shugaban kungiyar rajin kare hakkin mata ta Afrika mai suna women's Rights group Equality Now, wacce ke aiki da gwamnati, ta ce dokokin tsaron za su hada da bada kariya ga mata daga cin zarafi a makarantu. Jaridar Reuters ta ruwaito cewa kungiyar kare hakkin dan Adam din ta maka gwamnatin kasar Sierra Leone din a babbar kotun yammacin Afrika a 2018. A watan Disamba ne kotun ta yanke hukunci inda ta bi bayan kungiyar. Ta ce dokar kasar ta bayyana wariya tare da cin zarafi a kan hakkin yara mata.


LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




b

0 Response to "An cire dokar hana yara mata masu ciki zuwa makaranta a kasar Sierra-Leone"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?