--
Amurka Na Iya Zama Kasar Da Coronavirus Ta Fi Addaba - WHO

Amurka Na Iya Zama Kasar Da Coronavirus Ta Fi Addaba - WHO



Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), ta ce Amurka na iya zama kasar da cutar Coronavirus ta fi addaba nan ba da dadewa ba.

Mai magana da yawun hukumar lafiya ta duniyar, Margaret Harris, ta fadi a wani taron manema labarai a Geneva cewa, wannan hasashe na hukumar, ya biyo bayan dada yawa da sabbin kamuwa da cutar ke yi a Amurkar.

“Yanzu mu na ganin dimbin sabbin kamuwa da cutar a Amurka, saboda haka, Amurka na fuskantar yiwuwar samun kanta cikin wannan yanayi,” a cewar Margaret. Ta kara da cewa, “a halin yanzu, ba za mu iya cewa ko hakan zai faru ba, to amma akwai yiwuwar faruwar hakan.”
LATSA NAN👇👇👇 DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP  https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y



KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE DINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 




0 Response to "Amurka Na Iya Zama Kasar Da Coronavirus Ta Fi Addaba - WHO"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?