\ Almajiranci: Musulmai sun nemi gwamnati ta yi ma iyaye hukunci mai tsauri - BZGLOBALSERVICE.COM.NG Almajiranci: Musulmai sun nemi gwamnati ta yi ma iyaye hukunci mai tsauri - BZGLOBALSERVICE.COM.NG
Kutallata Hajarku Afarashi Maisuki, ________Mujallar BZGLOBALSERVICE.COM.NG________ Mujalla Ce Dake Watsa Labarai, Da Rohotanni, Labaran Nishadi, Bincike, Fadakarwa, Ilmantarwa Acikin Harshen Hausa, Kuma Acikin Awanni 24Hours Babu Qaqqautawa, Maziyartan Shafinmu Akowace Rana Basa Gaza Akallah Mutane Dubu biyar 5,000 Views Shafinmu Ya Shirya Tsaf Domin Karbar Tallace Tallace Daga Gareku Ma'abota Ziyartar Shafinmu Tallata Hajarka Adan Karamin Farashin Daya Fara Daga N1,000 Domin Bada Tallah Ko Qarin Bayani, Kutuntubemu Kaitsaye Ta Wadannan Numbobin: Kira: +2348133888333 Whatsapp: +2349066633320 Turo Mana Saqo Ta Adreshin Email: bzglobalservicelabari@gmail.com "Colour" <#20124d>
 • LABARAN YAU

  Monday, March 2, 2020

  Almajiranci: Musulmai sun nemi gwamnati ta yi ma iyaye hukunci mai tsauri  Wata kungiyar addinin Musulunci dake rajin kare hakkokin Musulmai, MURIC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki tsatstsauran hukunci a kan iyayen dake fatali da yayansu, musamman Almajirai mabarata. Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban MURIC, 

  Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyaa haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, a jahar Legas, inda yace tsarin hukunta iyayen zai sa su shiga taitayinsu game da tarbiyyar yaransu tare da basu kulawar da ta dace. 

  “Mun damu kwarai game da yawan yaran dake gararamba a kan tituna, wadannan su ne manyan gobe, yayanmu sune karfinmu, amma fa idan harm un basu tarbiyyar da ta dace ta hanyar ilimantar dasu, idan ba haka ba su zasu fitinemu.” Inji shi Akintola. 

  MURIC ta yi kira ga majalisar dokoki ta kasa da majalisun dokokin jaha su fara aikin samar da dokokin da zasu hukunta iyayen dake sakin yaransa sakaka, har ma ya kafa hujja da ayar Al-Qur’ani mai girma kamar haka; “A ciki sura ta 2, aya ta 233 na Al-Qur’ani mai girma,:

  Allah ya yi kira ga iyaye (musamman maza) su samar da muhimman bukatu kamar su abinci, wajen kwanciya, da kayan sawa, haka zalika Qur’ani ya tilasta ma iyaye su ilimantar da yaransu. “Don haka babban sakaci da hakkin yara a kan iyaye sakin yara suna barace barace a kan titi, talla ko kuma wani aikin wahala da sunan neman kudi, bugu da kari akwai batun haihuwar yara, Allah zai tambayi iyaye yadda suka kula da yaransu.” Inji shi. 

  Akintola ya koka kan yadda Musulmai suka yi mummunan fahimta ga ayar Qur’ani da ta bada daman kara aure, tare da mantawa da bukatar cewa har sai yana da ikon kulawa da sauran matan da yaransu kafin ya auro su. “Samuwar almajirai miliyan 10 a cikin babbar matsala ce, 

  tare da nuna alamun gazawar gwamnati, yaran nan dake gararamba a kan titi matsala ne a garemu, babu yadda za’a magance miyagun ayyuka ba tare da kiyaye kananan yara ba, kama yara ba shi bane, sai dai a kama iyayensu, a daure su.” Inji shi.


  LATSA NANπŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡ DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI TA WHATSAPP https://chat.whatsapp.com/BztTOlXx6c183yYthtZq1Y

  KU BIYOMU TA FACEBOOK FAGE FINMU KUYI LIKE DOMIN SAMUN LABARI 


  • Facebook Comments
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  KAYI TAMBAYA ANAN KOKA FADI RA'AYINKA AKAN ABINDA MUKEYI

  Item Reviewed: Almajiranci: Musulmai sun nemi gwamnati ta yi ma iyaye hukunci mai tsauri Rating: 5 Reviewed By: Admin