--
RUSHE MASALLACI A JIHAR RIBAS-- Tsohon Jagoran Tsagerun Niger Delta, Asari Dokubo Ya Caccaki Gwamna Wike

RUSHE MASALLACI A JIHAR RIBAS-- Tsohon Jagoran Tsagerun Niger Delta, Asari Dokubo Ya Caccaki Gwamna Wike

karya kake ka ce jihar Ribas ta Kiristoci ce, martanin Asari Dokubo ga Gwamna Wike
mu ne muka hada kudi muka sayi filin masallcin, cewaf Dokubo

Mujahid Dokubo-Asari ya fito fili a shafin sa na sada zumunta ya yi Allah wadai da abinda Wike ya aikata.

“Abinda ka aikata abin kunya ne, kuma bari na jaddada maka. Jihar Rivers ba ta kiristoci bace, kuma har abada ba za ta zama tasu ba. Karya kake yi kai ba ma Kirista bane''. Kalaman da Dokubo ga gwamnan Ribas.


Wannan ya biyo bayan rushe masallacin da gwamnan yayi ne, sannan ya fito bainar jama'a yace jihar ta kiristoci ce kuma bai san inda wani masallaci yake ba balle ace ya rusa.



A maida martain da Mr Dokubo ya yi ya ce, ''Indai da gaske ba masallacin to me ya kawo  ka wajen? Ni ɗin nan memba ne na Masallacin Trans-Amadi, a nan nake yin Sallolina tare da duk iyalina, don haka karya kake kace babu masallaci a wurin''.



Dokubo ya tabbatar da cewa su suka hada kuɗi suka sai filin masallacin a hannun Chief Edward Sotonye Amadi, kuma suna da takardun shaidar sayen wurin.




Tsohon tsageran na Niger Delta ya zargi gwamnan da salwantar da kudin jihar wajen daukar nauyin takarar Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, wanda shi musulmi ne, amma kuma saboda munafunci ya zo yana nuna kiyayya ga Musulmin jihar Ribas.



“Ka yi amfani da kudin Ribas ka ginawa kiristoci cibiyar ibada da kudin mu mun yi shiru ba mu ce komai ba, duk da muma a matsayin mu na 'yan jiha muna da hakki, saboda muma mun taimaka wajen gina wannan jihar''. Dokubo ke janyo hankalin Wike.



Yaci gaba da cewa ''Don haka wajibi ne Wike ya san cewa ba shi da ikon zabawa mutanen Rivers addinin da za su yi, kuma masallacin da ka rusa namu ne mu 'yan jiha, don haka ba za mu zura ido mu kyale ka ba''.



0 Response to "RUSHE MASALLACI A JIHAR RIBAS-- Tsohon Jagoran Tsagerun Niger Delta, Asari Dokubo Ya Caccaki Gwamna Wike"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?