--
Rufe Boda----Majalisar Zartarwar ECOWAS Ta Roki Nijeriya Da Ta Bude Iyakokinta

Rufe Boda----Majalisar Zartarwar ECOWAS Ta Roki Nijeriya Da Ta Bude Iyakokinta

Majalisar zartarwa ta kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ta roki gwamnatin Nijeriya da ta bude iyakokinta da ta rufe.
 Kakakin majalisar, majalisar Hon. Moustapha Cisse Lo, ya yi wannan kiran ne a taron majalisar zartarwar kungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma kashi na biyu da aka yi a Monrovia, Liberia.

Ya kara da cewa, rufe iyakokin ya zama barazana ga yarjejeniyar shiga da ficen da ke tsakanin kasashen. Kuma hakan yazo ne a lokacin da Afirka ke bukatar kokarin cire duk wani shinge tsakanin kasashenta. Cisse Lo, ya jawo hankalin gwamnatin Najeriya da ta kawo hanyar shawo kan shigo da kaya ba bisa ka'ida ba a maimakon kulle iyakokin.

Yace hakan ba hanya ce mai bullewa ba. "Rufe iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Benin wanda yafi wata daya da kuma rufe iyakar kasar Nijar babban kalubale ne game da amfanin kungiyar wajen kawo wanzuwar zaman lafiya da amana.

"Majalisar zartarwa ta ECOWAS na kira ga kasashen da su dage wajen bin dokar makwaftansu wajen fada da shigo da kayayyaki ba bisa ka'ida ba."

 "Dole ne a duba tushen matsalar nan don kawo karshenta na dindindin," inji shi. Kakakin majalisar

A karshe ya kara da kushe harin da 'yan kasar Afirka ta kudu ta ke kaiwa 'yan Nijeriya, ganin cewa hakan babbar barazana ce ga hadin kan Nahiyar Afirka.

0 Response to "Rufe Boda----Majalisar Zartarwar ECOWAS Ta Roki Nijeriya Da Ta Bude Iyakokinta"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?