--
Sanarwa Mai muhimmanci ga wadanda suka cike Neman Aiki A Hukumar Zabe ta Kasa Inec

Sanarwa Mai muhimmanci ga wadanda suka cike Neman Aiki A Hukumar Zabe ta Kasa Inec


Adireshin yanar-gizo na ɗaukar ma’aikata ba daga mu ba ne, INEC ta gargaɗi ƴan ƙasa

Hukumar zaɓe  mai zaman kanta ta ƙasa ta nesanta kanta daga wani adireshin yanar-gizo cewa ta na ɗaukar ma’aikata, wanda ke yawo a shafukan sada zumunta da sauran kafafe.

INEC, a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter da yammacin jiya Talata, ta bayyana adireshin yanar gizo: ‘inecnigeria gov service.site’ a matsayin na bogi 

“An ja hankalinmu kan wani sako na daukar ma’aikata na bogi da ake yadawa a kafafen sada zumunta daban-daban, da shafukan yanar gizo da ake yawan ziyarta da nufin damfarar ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.

“Mu na kira ga ƴan ƙasa da su yi watsi da wannan adirwshi na yanar gizo na ƙarya kuma su guji faɗa wa hannun ƴan damfara,” inji INEC.

Har ila yau, INEC ta ce ta lura cewa aikin daukar ma’aikata na wucin-gadi kyauta ne, yana mai cewa, “Ba a buƙatar biyan kowane nau’in kuɗi a duk lokacin aikin.

©️Ahmed El-rufai Idris

Kaduna State Coordinator Zumunta Youth Awarenesses Forum 🤝

0 Response to "Sanarwa Mai muhimmanci ga wadanda suka cike Neman Aiki A Hukumar Zabe ta Kasa Inec"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?