--
Matashin bakatsine yayi Wuff da Adama Matar Kamaye Ta Dadin Kowa Kalli Hotuna

Matashin bakatsine yayi Wuff da Adama Matar Kamaye Ta Dadin Kowa Kalli Hotuna


Fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Zahra’u Saleh wadda akafi sani da Adama matar Kamaye acikin wasan kwaikwayon nan na Dadin Kowa ta auri wani matashi dan asalin garin Dutsin-ma, dake a jihar Katsina.


Don tabbatar da gaskiyar labari, mujallar Fim ta ji ta bakin Hajiya Zahra’u Saleh, inda ta ce, “Wannan hotunan na biki ne wanda amarya da ango su ke ɗauka kafin biki, wato ‘prewedding’, amma kuma a cikin fim.


“Wallahi ba aure na yi ba. Wannan hotunan fim ɗi na ne wanda zai fito kwanan nan mai suna ‘Matar Yaro’. To sakamakon haka ne ya sa mu ka fara motsa jam’iyya da yaɗa manufar mu ta cikin wannan hoto da mu ka ɗauka sannan mu ka fara sakin sa duniya ta gani.”


Ta ƙara da cewa, “Fim ɗin zai kasance mai dogon zango kuma ni ce wacce na ɗauki nauyin shirya abu na da kai na.”


 

Jarumar ta yi farin cikin jin yadda ake ta yi mata fatan alheri. Ta ce, “Na ji matuƙar daɗi ganin yadda mutane su ka fara karɓar wannan fim tun kafin ya fito kasuwa. To hakan ya na nuna alamun kwalliya za ta biya kuɗin sabulu. Don haka su jira, nan ba da jimawa ba fim ɗin zai fito.”


Game da yadda masoyan ta su ke yi mata fatan ta yi aure, ta ce la shakka ta kusa yin auren.


Zahra’u ta ce, “Kamar yadda kowa ya ke ta magana, da man kuma ai duk ɗan aure ba ya ƙin aure, kuma shi aure ai lokaci ne, idan Allah ya kawo shi, aure da likkafani ai ba a tanadin su, ko da kuɗi ko babu idan Allah ya ƙadarta dole za ka yi shi.


Hotunan jarumar dai irin na zamani na mata da miji sun karade kafofin sadarwar zamani a yau din nan.








An ce sunan wanda ta aura din Mudassir Isyaku Dutsinma kuma matashi ne da ke cikin shekarun sa na samartaka.


Ita dai Adama Kamaye dai ta taba aure a baya amma shi sabon angon na ta ba mu da tabbacin ki saurayi ne ko kuma yana da mata.


Muna yi musu addu’a Allah yasa albarka a cikin auren nasu.

0 Response to "Matashin bakatsine yayi Wuff da Adama Matar Kamaye Ta Dadin Kowa Kalli Hotuna "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?