--
 Kalli Hotunan manyan gidajen Mai kamfanin Facebook masu darajar N131b

Kalli Hotunan manyan gidajen Mai kamfanin Facebook masu darajar N131b

Mamallakin Facebook, Mark Zuckerberg, yana matukar kaunar harkar gidaje da mallakarsu, hakan yasa yake da gidaje a birane Mutum na biyar da yafi kowa arziki a duniya yana alfahari da kadarorin da yake dasu da suka kai N131 biliyan da sauran manyan gidajensa 


Gidan da yake zama tare da matarsa da 'ya'yansa na da girman kafa 5,617, dakunan bacci 5 da kuma sauran abubuwan kayatarwa Mamallakin Facebook, Mark Zuckerberg yana daya daga cikin jama'a masu son tara kadarori. 



Duk da 'ya'yansa biyu kacal masu shekaru 3 da 5, biloniyan yana da jerin katafaren gidaje da kadarori masu yawa da ya siya da sunansa. Palo Alto, California mai darajar $50 miliyan (N20.5 billion) Katafaren gidan Palo Alto dake California yana daya daga cikin gidajen da Zuckerberg yake kauna kamar yadda NYpost ta ruwaito. 


Wannan kyakyawan gidan an gano cewa dan kasuwan ya siye shi ne shekara daya kafin ya auri matarsa. Kamar yadda Architectural Digest suka ruwaito, ya siya gidan kan kudi $7 miliyan kuma yana da dakunan bacci 15 da bandakuna sama da 16. Gidan yana da fadin taku 20,000 kuma yana da wurin wanka da sauran ababen more rayuwa. Lake Tahoe, California mai darajar $59 miliyan (N24.1 biliyan) 


Zuckerberg na kaunar California a bayyane saboda gidan da ya mallaka a Lake Tahoe. Gidan hutun an gina shi ne a kusan aka 10 kuma yana da darajar N24.1 biliyan, ya siye shi a 2018. Gidan mai girman kafa 5,322 yana da dakunan bacci shida, bandakuna biyar, tafki mai fadin kafa 400, dakin baki da garejin mota, Permit records suka tabbatar. 


Source: Legit 

DAGA BZ NEWS 24/7

1 Response to " Kalli Hotunan manyan gidajen Mai kamfanin Facebook masu darajar N131b "

  1. Enter your comment...gaskiya ina matukar jin dadin labaran BZnews

    ReplyDelete

Tell us what you think about this article?