--
Damfarar N25.7b: Kotu ta yankewa tsohon MD fitaccen banki shekaru 12 a gida yari

Damfarar N25.7b: Kotu ta yankewa tsohon MD fitaccen banki shekaru 12 a gida yari


Wata kotun Ikeja ta yankewa tsohon manajan daraktan tsohon Bank PHB, Francis Atuche, shekaru 6 a gidan yari kan satar N25.7 biliyan 


Kotun ta sake yankewa tsohon CFO, Ugo Anyanwu hukuncin shekaru shida a gidan gyaran hali duk a kan laifin 


Mai shari'a Lateefat Okunnu wacce ta shugabanci kotun ta ce EFCC ta tabbatar mata da cewa sun saci kudin ne ba bashi suka karba ba kamar yadda suke ikirari


Ikeja, Legas Francis Atuche, tsohon manajan daraktan tsohon bankin PHB Plc, ya samu hukuncin shekaru shida a gidan yari kan damfarar makuden kudade har N25.7 biliyan. 


Mai shari'a Lateefat Okunnu ta babbar kotun dake Ikeja a ranar Laraba, 16 ga watan Yuni ta hada da tsohon jami'in kudi na bankin, Ugo Anyanwu shekaru shida a kan laifin, Premium Times ta ruwaito. 


Legit.ng ta tattaro cewa alkalin ta sallama tare da wanke matar Atuche mai suna Elizabeth. A yayin yankewa su biyun hukunci, mai shari'ar ta ce EFCC ta tabbatar da kokenta kuma babu shakka hakan ya faru sama da shekaru 10 da suka gabata. 


Sace N25.7b aka yi ba bashi ba Tsohon shugaban bankin, matarsa da Anyawu aka zarga da sacewa tare da hada kai wurin watanda da N25.7 biliyan na bankin.l 


An gurfanar dasu a 2011 a gaban Okunnu amma basu amsa laifin da ake zarginsu da shi ba. Amma kuma yayin karanto hukuncin, alkalin ta tabbatar da koken EFCC na cewa sace kudin aka yi ba bashi aka karba ba kamar yadda Atuche yace, The Cable ta ruwaito. 

0 Response to "Damfarar N25.7b: Kotu ta yankewa tsohon MD fitaccen banki shekaru 12 a gida yari "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?