--
Sabon Salo: Sowore ya bayyana a kotu tare da bokansa ana tsaka da shari'a duba dalili

Sabon Salo: Sowore ya bayyana a kotu tare da bokansa ana tsaka da shari'a duba dalili


Dan siyasa kuma mai kafar yada labarai ta yanar gizo, Sahara Reporters, Omoyele Sowore, an yi masa rakiya zuwa Kotun Majistare da ke Wuse Zone 2, Abuja, a ranar Talata tare da wani mutum sanye da riga mai launin ja da baki mai tsayo zuwa gwiwa da hularta.


Mutumin, wanda bai bayyana sunansa ba, yana daga cikin magoya bayan Sowore da ke kotun don shaida yadda ake gudanar da shari’arsa, tare da wasu mutum hudu, kan tuhume-tuhume uku da suka hada da hada baki, hada taro ba bisa doka ba da kuma tunzura jama’a. 


An bayyana mutumin a matsayin bokan Sowore, The Nation ta ruwaito. 


Rigar sa tana dauke da wani kayan ado da bawon katantanwa da karamin kan dila da akayi zane akai. Yana dauke da sanda da karamar wutsiyar shanu rike a hannun damansa; Yana kuma rataye da jan buhu mai zane a kafadarsa. Mutumin yana da alamun alli kewaye da idanunsa kuma bai sanya takalmi ba. 


Bayyanar sa a bakin kotun ya haifar da kallo tsakanin mutane a kewayen harabar kotun. Kamar sauran wadanda suke tare da Sowore, mutumin, wanda ya yi kama da mai duba a fina-finan Ibo, an ba shi izinin shiga kotun.


A yayin shari'ar, wani mai gabatar da kara, jami'in 'yan sanda, ya ba da shaida game da yadda aka kama wadanda ake tuhumar da sanyin safiyar 1 ga Janairun 2021 yayin da ake zarginsu da yin taro ba bisa ka'ida ba da tayar da hankalin jama'a. Shaidan ya ce, rundunar ‘yan sanda ce ta cafke wadanda ake zargin a mahadar Lokogoma da ke Abuja. 


Yayin da lauyan da ke amsa tambayoyin wadanda ake tuhumar, Marshal Abubakar, mai shaida ya ce shi da kansa bai kama Sowore ba, amma shi memba ne na tawagar da ta yi nasarar cafke dukkan wadanda ake tuhumar. 


Kafin dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 7 ga Mayu na wannan shekarar, Alkalin ta banbanta sharuddan da aka gindaya a kan belin da aka ba wadanda ake tuhuma na biyu zuwa na biyar ta hanyar ba su izinin yin tafiya zuwa wajen Abuja. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Sabon Salo: Sowore ya bayyana a kotu tare da bokansa ana tsaka da shari'a duba dalili"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?