--
Kashe Mutanen Arewa: Duk laifinku ne, Sanata Ahmad Lawan ya caccaki gwamnonin Yarbawa

Kashe Mutanen Arewa: Duk laifinku ne, Sanata Ahmad Lawan ya caccaki gwamnonin Yarbawa


Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ranar Asabar ya caccaki gwamnonin kudu maso yamma, inda ya daura musu alhakin kashe-kashen da ya faru a kasuwar Shasha a Ibadan, jihar Oyo. 


A cewar Lawan, gwamnonin ne suka tunzura matasan yankin wajen kaiwa yan Arewa hari. 


A hirar da yayi da jaridar BBC Hausa, Lawan ya ce kiran da wasu gwamnonin kudu maso yamma keyi na korar Fulani daga yankin ya haifar da hakan. 


Hakazalika, yace kalaman gwamnonin ya haddasa hare-haren da ake kaiwa yan Arewa a kudancin Najeriya.


"Abinda ya faru a jihar a Oyo, da kuma abubuwan da suk adan faru a wasu jihohin kudu maso yammacin Najeriya, watakila da kudu maso gabashi, an samu matsalan shugabancin," Yace.


Gwamnonin suke ke da hakki muhimmi don kare mutanen dake yankinsu." "Kuma irin kalamai da wasu gwamnoni sukayi, musamman daga wannan yankin ya taimaka wajen tunzura mutanen yan asalin jihohin, wadanda ke ganin ai shugabanninsu sun basu lasisi ne." 


Zaku tuna cewa a ranar 18 ga Febrairu, rikici ya barke a Shasha sakamakon rashin fahimta tsakanin wasu kuma yayi sanadiyar rashin rayuka da dukiyoyi. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Kashe Mutanen Arewa: Duk laifinku ne, Sanata Ahmad Lawan ya caccaki gwamnonin Yarbawa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?