--
Inyamurai da yarabawa sun yi wa Dr. Gumi kaca-kaca  duba abinda suka ce

Inyamurai da yarabawa sun yi wa Dr. Gumi kaca-kaca duba abinda suka ce


Shugabannin kungiyoyin kudu da yankunan jihohin tsakiya, a ranar Alhamis sun cacaka Sheikh Ahmad Gumi kan cewa yan bindiga suna fada ne saboda rashin adalcin da Nigeria ta yi wa arewa, Vanguard ta ruwaito.


A cikin wani sanarwa ta suka fitar mai taken 'Gumi ya yaye gyalen', kungiyar ta tambayi Gumi kacewa shin ko Hausawa na zanga-zanga kan rashin adalcin da Fulani ke musu da sauran yan Nigeria'. 


Sanarwar na dauke da sa hannun Yinka Odumakin (Kudu maso Yamma), Cif Guy Ikokwu (Kudu maso Gabas), Sanata Bassey Henshaw (Kudu maso Kudu) da Dr. Isuwa Dogo (Middle Belt). 


Wani sashi na sanarwar ya ce: "Kungiyar shugabannin kudu da jihohin tsakiya ba ta yi mamakin yadda Sheikh Gummi ya nuna kansa a AIT da safen yau, inda ya ke neman a yi wa yan bindigan da ya ce arewa suka nema wa hakkinta afuwa. 


"Daga cikin rashin adalcin tabbas akwai zaben Buhari a matsayin shugaban kasa sau biyu duk da cewa kasar nan na bukatar shugaba mai lura da kula da abinda ke faruwa. "Kusan tsawon shekaru shida kasar na cigaba da tsindumawa cikin matsaloli da suka hada da son kai da mulkar kasar kamar Jamhuriyar Fulani. 


"Daga cikin rashin adalcin da ake yi wa Arewa akwai kashe mutane da makiyaya ke yi a sassan Nigeria a yayin da gwamnati ke kare su tare da rangwanta musu da nuna son kai a fili da shugaban kasa ke yi."


Kungiyoyin, cikin sanarwar ta cigaba da yi wa Sheikh Gummi shagube na nuna cewa Arewa ne ke amfana da albarkatun kasa da kudanci ke samarwa tare da cewa Gummi na nema wa Fulani afuwa. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "Inyamurai da yarabawa sun yi wa Dr. Gumi kaca-kaca duba abinda suka ce"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?