--
An lalata kadarori a rikici kan nadin sabon sarkin Billiri Kalli Hotuna

An lalata kadarori a rikici kan nadin sabon sarkin Billiri Kalli Hotuna


Rikicin ya biyo bayan zanga-zangar da wasu kungiyoyi suka yi ne wadanda ke zargin gwamnatin da rashin adalci a tsarin zaben sabon Mai Tangale a Billiri. Hakanan akwai rikicin addini yayin da aka kona wuraren bautar musulmai a yankin na Billiri. 


Amma a wani labarin, Inuwa Yahaya, gwamnan jihar, ya ce tsarin nadin sabon basaraken ya kasance a bayyane, kuma tashin hankalin ya faru ne daga wadanda ke son shafa wa gwamnati bakin fenti don ta zabi wani dan takararsu. 


Kafin a a sanar da wanda gwamnan jihar ya zaba, wasu daga cikin mazauna yankin suka fara zanga-zangar nuna su dole a nada musu zabinsu; wanda daga bisani ya jawo tashin hankalin da ya kai ga tsare hanyar Gombe zuwa Adamawa tare kone-konen masallatai da shaguna. 


Gwaman jihar ta Gombe ta fito yayi bayanin halin da ake ciki tare da bayyana matakin da ya dauka dangane da lamarin. Yake cewa: "Ya ku 'yan uwana, duk kuna sane cewa bayan rasuwar Mai Martaba, marigayi Abdu Buba Maisheru II, kuma daidai da dokokin da al'adun da muka shimfida, mun sanya ayyukan zabar sabon Mai Tangle," in ji shi,



“Tsarin, wanda ya kasance a bayyane kuma ba tare da wata tsangwama ba, ya haifar da tura mutane uku da aka ba da shawara ta hanyar sarakunan gargajiya na Tangale, daga cikinsu zan zabi dan takarar da zai cike kujerar Mai Tangle kamar yadda doka ta tanada.


" Gwamnan ya ce batun maye gurbin wani al'amari ne na Tangale tare da jihar Gombe kuma dukkanin wadannan mutane ukun da aka ba da shawarar sun cancanci sarautar Tangale ne saboda nasabarsu da masarautar Mai Tangale. 


Ya ce ta hanyar tarihi, kuma kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada, addini ba shi ne mizani ba wajen zaben sabon Mai Tangale ko wani ofishin gwamnati game da hakan. Gwamnan ya kuma sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankin don dakile yaduwar rikici. Ya ce gwamnati na rufe duk wani shawara kan sabon Mai Tangale har sai yadda al'amuran suka daidaita ga al'ummomin da abin ya shafa. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "An lalata kadarori a rikici kan nadin sabon sarkin Billiri Kalli Hotuna"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?