--
An damke matashiya 'yar 17 da bindiga a makaranta ta bayyana cewa ita 'yar kungiyar aisiri ce kuma tazo kashe malaminta ne duba dalili

An damke matashiya 'yar 17 da bindiga a makaranta ta bayyana cewa ita 'yar kungiyar aisiri ce kuma tazo kashe malaminta ne duba dalili


Matashiyar dalibar da aka kama da bindiga a makaranta ta amsa cewa tana cikin kungiyar yan asiri. Ta kuma ce a wurin saurayinta, Okon Effingham, wanda ke da aure da yara shida ta karbo bindigar, rahoton jaridar Vanguard.


Da farko an yi ikirarin cewa dalibar, yar makarantar sakandare ta gwamnati na Ikot Ewa, jihar Rivers ta tafi da bindigar makaranta ne domin harbin malaminta da ya ce ta aske gashinta da ta rina. 


Amma bayan kama ta, yan sanda sun gano cewa za ta kai bindigan wurin wani makeri ne. Ta shaidawa manema labarai a ranar Juma'a 19 ga watan Fabrairu yayin da ake holen ta tare da saurayinta wanda suka fara soyayya tun Agustan 2020 cewa shine ya mallaki bindigar. Ta kara da cewa mutumin yana taimaka mata da wasu abubuwa amma ba shi ke biyan kudin makarantar ta ba. 


Ta ce mahaifiyarta na barin mutumin ya kwana a dakinta inda ya zo gidansu ziyara. Da ta ke magana a hedkwatar yan sanda, Diamond Hill, Calabar, yayin holen ta da saurayinta wanda ya mallaki bindigar wasu 11 domin aikata laifuka, ta ce, 


"Ni yar kungiyar asiri na Sky Queen ne, bani da mukami a kungiyar, na san wanda ya mallaki bindigar tun bara, ya kan zo gidan mu ya kwana kuma ya kan taimaka min da kananan abubuwa, amma ba shi ke biya min kudin makaranta ba." 


A bangarensa, saurayin yar makarantar, Okon Effiong ya ce, "Ina da aure da yara shida, ban bata bindigar ba, dauka ta yi da kanta daga karkashin gado inda na ajiye." Ya kuma ce suna soyayya kuma mahaifiyarta ta sani domin yana da nufin aurenta. 


Kwamishinan yan sandan jihar Cross River, Sikiru Akanda ya ce za a cigba da zurfafa bincike sannan ya yi kira ga iyaye su rika kusantan yaransu don sanin wadanda suke harka da su. 


DAGA BZ NEWS 24/7

Domin sauke manhajar labaran Bz News24/7 a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=bz.globalservice7

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: 

Facebook:https://web.facebook.com/bzlabari24 

Twitter: https://twitter.com/bzglobalsevice

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: 

bzglobalservicelabari@gmail.com

0 Response to "An damke matashiya 'yar 17 da bindiga a makaranta ta bayyana cewa ita 'yar kungiyar aisiri ce kuma tazo kashe malaminta ne duba dalili"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?