--
'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kano sun jikkata mutum daya da kwace motarsa,

'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kano sun jikkata mutum daya da kwace motarsa,


Wasu 'yan bindiga sun firgita jama'a bayan sun yi harbe-harbe kafin daga daga bisani su kwace wata mota 


'Yan bindigar sun fito da mai motar ta karfin tuwo sannan suka harbe shi kafin su gudu da ita 


Kakakin rundunr 'yan sandan jihr Kano, DSP Abdullahi Kiyawa, ya ce an samu motar bayan bin sahun 'yan ta'ddar Wasu 'yan bindiga sun yi harbe-harbe tare da tarwatsa jama'a a daidai katafaren shagon Ado Bayero Mall da ke kan titin zuwa gidan Zoo a birnin Kano. 


Freedom Radio ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe goma na daren ranar Asabar. A cewar rahoton da Freedom Radio ta wallafa, 'yan bindigar sun yi harbe-harbe a sararin samaniya, 


lamarin da ya saka jama'a gudun neman mafaka. 'Yan bindigar sun nufi wata inda suka fito da mutumin da ke ciki tare da harbinsa nan take kafin su gudu da motar. 


Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar wa da Freedom Radio faruwar lamarin tare da sanar da cewa sun kai mutumin da aka harba asibiti. 


Kazalika, ya bayyana cewa 'yan sanda sun dauko motar da 'yan bindigar suka kwata bayan sun gudu sun barta sakamakon matsin lamba daga jami'an 'yan sanda da ke kokarin cin musu. 

0 Response to "'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kano sun jikkata mutum daya da kwace motarsa, "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?