--
'yan sanda sunyi min duka har'saida yasa ni fitsari a wando, -Cewar wata Budurwa

'yan sanda sunyi min duka har'saida yasa ni fitsari a wando, -Cewar wata Budurwa


Da 'yan sanda suka fara dukana kamar bakuwar karya, sai da na fita hayyacina na tsula fitsari, cewar wata Felicia 



A cewarta, wasu 'yan sanda da ke Surulere, jihar Legas, sun azabtar da ita matuka don ta sha duka da naushi 


Ta ce ta daga waya tana daukar bidiyon zanga-zangar EndSARS, hakan ne ya fusata 'yan sanda suka hau dukanta Felicia Okpara, ta ce 'yan sanda sun cutar da ita


saboda ta daga waya tana daukar bidiyon zanga-zangar EndSARS da matasa suka yi a Surulere da ke jihar Legas. 


A ranar Juma'ar da ta gabata, Okpara ta kai korafinta gaban kwamitin bincike na cin zarafin 'yan sanda na jihar Legas, Channels TV ta wallafa. 


A cewar Okpara, ta gama wata tattaunawa kenan, sai ta dauki hanyar tafiya gida, da ta ga ana zanga-zangar, sai ta shiga. 


Bayan nan ne sai taji harbi, kowa ya fara gudun neman tsira. Kamar yadda tace, ta gudu gefen wani ofishin 'yan sanda, sai ta ciro wayarta ta fara daukar bidiyo, sai ga wani dan sanda ya gabato ta. 


Ya fara umartar ta da ta daina daukar bidiyon, ita kuma ta ki dainawa. Sai ya ciro bindiga ya ja ta cikin ofishin 'yan sandan tare da wata mata. Su na isa ciki, sai 'yan sanda har da mata suka hau dukansu suna naushinsu. 



A cewarta, da taji shigar duka har fitsari ya kubuce mata. "Da naji azaba, sai wayata ta fadi kasa, daya daga cikin 'yan sandan ya taka wayar saboda a tunaninsa zan sanya bidiyon abinda na dauka a yanar gizo ne," a cewarta. 


"Tun muna bakin ofishin, 'yan sanda suka fara tururuwar fitowa suna dukanmu suna janmu cikin ofishin suna naushinmu," Okpara tana maganar tana zubar da hawaye. 


SOURCE: LEGIT

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A WHATSAPP:

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI A TELEGRAM:


KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app75765

0 Response to "'yan sanda sunyi min duka har'saida yasa ni fitsari a wando, -Cewar wata Budurwa "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?