'Yan sanda sun bi matar da ta yadda N115,000 ba tare da sani ba, sun kai mata
'Yan sanda masu taimakon gaggawa sun bi wata mata har gida, inda suka mayar mata da jakarta - Jakar matar mai cike da makudan kudade da wayarta ta fadi daga kan babur ba tare da ta sani ba
'Yan sandan sun nemi sanar da dan acaban da ke tuka ta amma abin ya ci tura Kungiyar 'yan sanda masu taimakon gaggawa (RRS) na jihar Legas ta sanar da yadda jami'anta suka samu nasarar ceto jakar wata mata mai cike da makudan kudade, kuma suka maida mata.
A cewarsu, jami'an RRS suna cikin sintiri wuraren Igando, sai suka hangi jakar wata mata ta fado daga babur. Sun dauka har suka nemi sanar da dan acaban da yake tuka ta amma abin ya ci tura. Take a nan suka bi bayansu, har sai da suka tabbatar sun mayar wa da matar jakarta.
...then handed it over to her. She confirmed the sum of N115,000 and a Tecno phone inside the purse were all intact. #TheGoodGuys pic.twitter.com/Ha3VdvmkMe
— Lagos State Police Command II (@rrslagos767) November 19, 2020
Sun wallafa hotunan wasu jami'an suna mika wa wata mata jaka, inda su ka wallafa a shafinsu na Twitter:
"Jami'an RRS suna cikin sintiri da yammacin nan wuraren Igando, sai suka hangi wata jar jaka ta fado daga babur. Sun dauki jakar, har su ka nemi sanar da dan acaban, amma ya yi tunanin tsare shi za su yi sai ya gudu.
"A hankali su ka bi bayansa, har inda matar za ta sauka, suka mika mata jakarta. Sai da ta kirga kudinta na cikin jakar N115,000 da wata waya kirar Tecno a cikin jakar. Babu abinda ya bata."
SOURCE: LEGIT.NG
0 Response to "'Yan sanda sun bi matar da ta yadda N115,000 ba tare da sani ba, sun kai mata "
Post a Comment
Tell us what you think about this article?